Balo-balo: Abba Kyari ya tono batutuwa, ya fadi gaskiyar alakarsa da Hushpuppi
- DCP Abba Kyari na yin wata magana da ke nuna alamar damarsa ta karshe don hana a mika shi ga Amurka domin gurfanar da shi gaban kuliya
- Dan sandan da aka dakatar ya fadawa babbar kotun tarayya a ranar Alhamis, 2 ga watan Yuni cewa kada ta bari gwamnatin tarayya ta yi yunkurin mika shi Amurka
- A bangare guda, ya bayyana gaskiyar alakar da ke tsakaninsa da Hushpuppi da ake tsare dashi kan wata damfara
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja – Mataimakin kwamishinan ‘yan sanda da aka dakatar, Abba Kyari, ya yi zargin cewa matakin da ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya ya dauka na mika shi kasar Amurka, ba shi da amfani ga shari’a, kana ya yi bayanin alakarsa da Hushpuppi
A daya daga cikin sabbin kararrakin da aka shigar a babban kotun tarayya da ke Abuja, Kyari a ranar Alhamis, 2 ga watan Yuni, ya bukaci mai shari’a Inyang Ekwo da kada ya amince da tasa keyar sa zuwa Amurka domin fuskantar shari’a kan hannu a wata damfara.
Ya yi zargin cewa shirin mika shi Amurka domin gurfanar da shi ba komai bane face nufin hukunta shi, inji rahoton Vanguard.
Da yake bayyana cewa kama shi da tsare shi yana da wasu manufofin siyasa, babban jami’in ‘yan sandan ya yi ikirarin cewa mika shi zuwa kasar waje zai dakushe kungiyoyin laifuffuka daban-daban da tawagarsa ta IRT ke yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yace:
“A gaskiya na san cewa laifuffukan da aka fada a siyasance ne kawai kuma an yi su ne da nufin gurfanar da wanda ake kara da hukunta shi saboda kabilarsa, kasarsa, kuma ba a gina shi kan gaskiya ba, kuma ba a gina shi kan adalci ba."
A bayyane, Kyari ya ce ba komai bane ke tattare da batun tuhume-tuhumensa sai dai ganin an dakushe ayyukan da yake yi na ragargazar kungiyoyin ta'addanci.
Abinda ke tsakani na da Hushpuppi - Abba Kyari
Abba Kyari, ya yi magana game da alakarsa da, Abbas Ramon (Hushpuppi) da ake zargi da damfarar wani balarabe a kasar Qatar, injir rahoton The Nation.
Kyari ya ce alakarsa da Hushpuppi ta fara ne a lokacin da yake tare da shi, a matsayinsa na babban jami’in ‘yan sanda, a wani samame watanni biyar kafin a kama shi Hushpuppin.
Kotu za ta ci gaba da sauraran batun mika Abba Kyari Amurka
A wani labarin, wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta sa ranar Juma’a za ta ci gaba da sauraren karar mika ACP Abba Kyari da aka dakatar zuwa hannun Amurka, The Nation ta ruwaito.
Mai shari’a Inyang Ekwo ya zabi ranar ne a ranar Alhamis domin baiwa babban lauyan gwamnati damar shigar da kara a hukumance a kan batun da Kyari ya shigar na kin amincewa da matakin farko na kalubalantar cancantar mika shi da AGF ya shigar.
AGF ya nemi kotu ta ba ta izinin mika Kyari ga hukumomin Amurka dangane da alakarsa da wanda ake zargi da damfara ta yanar gizo, Abbas Ramon (wanda aka fi sani da Hushpuppi).
Asali: Legit.ng