Kaduna: 'Yan sanda sun bindige 'yan bindiga 2 yayin dakile sabon farmakin da suka kai
- Rundunar 'yan sandan Jihar Kaduna ta mayar da wani hari da 'yan bindiga su ka kai karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar
- Kakakin rundunar ta jihar Kaduna, Mohammed Jalige ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarda da ya saki ranar Alhamis
- Ya ce a ranar Talata 'yan sandan su ka gano an kai harin kauyen Kimdi, hakan ya sa su ka dakile harin wanda su ka halaka 'yan ta'adda biyu
Kaduna - Rundunar 'yan sandan Jihar Kaduna ta samu nasarar dakile wani hari da 'yan bindiga su ka kai karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar.
Mohammed Jalige, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarda da ya saki ranar Alhamis, TheCable ta ruwaito.
Ya ce rundunar ta gano yadda su ka kai harin kauyen Kimdi da ke karamar hukumar Birnin Gwari ranar Talata, hakan ya sa su ka kai wa 'yan bindigan samame inda su ka halaka 'yan ta'adda biyu tare da kwace bindiga kirar AK 47.
Ya ci gaba da cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Yayin kokarin ganin bayan ta'addanci a jihar Kaduna, musamman a wuraren Birnin Gwari, rundunar 'yan sanda a ranar Talata, 31 ga watan Mayu ta kara samun wata nasarar.
"Ta samu nasarar halaka 'yan bindiga biyu inda ta kwace AK-47 a hannunsu, yayin da ta raunata wasu 'yan bindigan da yawa.
"Wannan ya biyo bayan labarin da ta samu a ranar da misalin karfe 4 na yamma, akan yadda wasu 'yan ta'adda da dama su ka kai hari kauyen Kimdi da ke karamar hukumar Gwari.
"Take a nan rundunar ta tura jami'ai mafi kusa zuwa wurin don mayar da hari inda su ka dinga musayar wuta har su ka samu nasarar halaka 'yan bindiga biyu tare da kwace bindigogi biyu kirar AK-47."
Ya ci gaba da bayyana yadda hukuma ke sane da matsalolin tsaron yankin musamman bangaren Birnin Gwari kuma gwamnati da jami'an tsaro su na iyakar kokarinsu wurin ganin sun kawo karshen ta.
Ya kara da cewa za su tabbatar sun tsare rayuwar jama'a da dukiyoyinsu matukar iyawarsu.
Ƴan ta'addan ƙasar Kamaru sun shigo Najeriya, sun bindige rayuka 20
A wani labari na daban, tsagerun Ambazonia, wata kungiyar 'yan aware ta kudu maso yammacin kasar Kamaru, ta halaka rayuka a kalla 20 a cikin al'ummar karamar hukumar Boki ta jihar Cross River a Najeriya.
Chief Cletus Obun, tsohon dan majalisar jihar Cross River kuma dan takarar kujerar majalisar wakilai ta Boki da Ikom ne ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce lamarin ya faru ranar Lahadi.
Asali: Legit.ng