Da duminsa: Nakiya ta sake tashi a gidan giya yayinda yan PDP ke murnar nasarar Atiku

Da duminsa: Nakiya ta sake tashi a gidan giya yayinda yan PDP ke murnar nasarar Atiku

  • Karo na biyu a watan nan kadai, an sake samun tashin Bam a mashaya a jihar Kogi, Arewa maso tsakiyar Najeriya
  • Tashin bama-bamai a gidajen shakatawa a Arewacin Najeriya wani sabon abu ne da aka fara kwanan nan
  • A makonnin da suka gabata, an kai ire-iren wadannan hare-hare jihar Taraba da kuma jihar Yobe

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kabba- Kuma dai, an kai harin Bam karamar hukumar Kabba dake jihar Kogi, kwanaki 18 kacal da kai harin farko.

Leadership ta ruwaito cewa wannan karon ana zargin nakiya ce ta tashi a wani gidan giya dake Okepadi, yayinda mambobin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ke murnar nasarar Alhaji Atiku Abubakar a zaben fidda gwanin dan takaran shugaban kasa.

Wannan annobar ta auku ne ranar Lahadi, 29 ga watan Mayu, 2022.

Kara karanta wannan

Shirin zaben fidda gwani: Tinubu, wasu 11 sun tsallake tantancewar shugabannin APC

Taswira
Da duminsa: Nakiya ta sake tashi a gidan giya yayinda yan PDP ke murnar nasarar Atiku

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Willian Aya, wanda ya tabbatar da labarin yace abin ya faru ne a mashayar Omofemi, Okepadi, Kabba, misalin karfe 9:15 na dare.

Yace har yanzu dai ba'a san adadin wadanda abin ya shafa ba amma ana gudanar da bincike kan tashe-tashen abubuwa a Kabba.

Aya yace:

"Wadannan yan ta'addan cikinmu suke; makwabtanmu ne a mashayar, a kasuwanni, wuraren cin abinci, bankuna kuma tare dasu muke harkokin tafiye-tafiye."

Aya ya yi kira ga jama'ar gari su baiwa hukuma bayanin duk wanda suka gani da kayan hada bama-bamai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel