Bayan kwanaki 7, an fara kama wadanda ake zargi da fille kan ‘Dan Majalisa a Anambra

Bayan kwanaki 7, an fara kama wadanda ake zargi da fille kan ‘Dan Majalisa a Anambra

  • Har yanzu ana makokin Hon. Okechukwu Okoye wanda ‘yan ta’adda ne suka yi masa kisan gilla
  • Rade-radi ya zagaye gari cewa dakarun jami’an tsaro sun kama wanda ake zargi da laifin kisan
  • An kama wani Nnahadi Michael a Ebenator-Udene da ake zargi da hannunsa wajen kashe Okoye

Anambra - Daya daga cikin wanda ake zargi da hannu wajen kisan Hon. Okechukwu Okoye ya shiga hannu. Vanguard ta fitar da wannan rahoto yau da safe.

Yau kusan mako daya kenan da aka samu wasu miyagun ‘yan bindiga da suka hallaka, ‘dan majalisar dokokin jihar Anambra, Honarabul Okechukwu Okoye.

Jami’an tsaro sun yi nasarar cafke wani mai suna Nnahadi Michael, wanda shi ake zargin yana da hannu wajen datse kan wannan Bawan Allah saboda zalunci.

An yi ram da Nnahadi Michael ne a jiya a garin Amichi, karamar hukumar Nnewi, jihar Anambra.

Kara karanta wannan

Innalillahi: ‘Yan bindiga sun bindige tsohon kwamishina, sun sace ‘ya’yansa mata

Wanda ake zargin ya taya Micheal wannan danyen aiki wani malamin tsibbu ne. Yanzu haka jami’an tsaro sun bazama domin kama wannan boka a fadin jihar.

Rahoton ya bayyana cewa an rusa gidan bokan, yayin da shi kuma wanda aka kama yana hannun ‘yan sanda inda yake amsa tambayoyi a binciken da ake yi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamnan Anambra
Gwamnan Anambra, Charles Soludo Hoto: www.inlandtown.com
Asali: UGC

'Yan sanda ba su ce komai ba

Mai magana da yawun bakin ‘yan sanda na Anambra, Tochukwu Ikenga bai iya tabbatar da labarin kama wannan mutumi ba, duk da maganar ta shiga ko ina.

Idan labarin da mu ke samu gaskiya ne, wanda aka kama ya amsa cewa sun hallaka wasu ‘yan siyasa uku, daga ciki har da shi ‘dan majalisar da suka yankawa kai.

A wani kaulin, rundunar jami’an tsaron Najeriya sun kama Nnahadi Michael ne a ranar Lahadi da kimanin karfe 1:35 na rana a wani kauye da ake kira Ebenator-Udene.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama yan yankan aljihu 10 a wajen zaben fidda dan takarar shugaban kasa na PDP

Leadership ta ce da aka kama wannan mutumi a Ebenator-Udene, ya fadawa hukuma cewa shugabansu da ya jagoranci kashe ‘dan majalisar dokokin ya mutu.

Kafin rasuwar Marigayin, shi ne mai wakiltar mazabar Aguata II a majalisar dokokin jihar Anambra. Daga yankinsa ne Gwamna Farfesa Charles Soludo ya fito.

'Yan bindiga su na barna

Yayin da al’ummar garin Aguata su ke makokin mutuwar Okechukwu Okoye, sai aka ji wani labari wanda ya fi na kisan zaluncin da aka yi masa tada hankali.

Kun samu rahoto cewa miyagun ‘yan bindigan da ake zargi da laifin kashe Hon. Okechukwu Okoye, sun ce za su cigaba da hallaka wasu ‘yan siyasar Anambra.

Asali: Legit.ng

Online view pixel