Yanzu-Yanzu: Jami'an tsaro sun budewa magoya bayan Okorocha wuta a farfajiyar gidansa
- Jami'an tsaro a halin yanzu sun bude wa magoya bayan Sanata Rochas Okorocha wuta a farfajiyar gidansa da ke Abuja
- Magoya bayan da yawancinsu mata ne da manema labarai a halin yanzu sun cika bujensu da iska domin gudun ceton rayukansu
- Jami'an tsaro sun zagaye gidan fitaccen dan siyasan in da suka jaddada cewa ba za su bar wurin ba har sai sun cafke shi
FCT, Abuja - Jami'an tsaro da ke zagaye da gidan tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, a Abuja sun bude wa magoya bayan dan majalisar wuta domin tarwatsa su.
Masu zanga-zangar wadanda da yawansu mata ne da manema labarai da ke kula da cigaban, a halin yanzu suna gudun ceton rayukansu.
Jami'an tsaron suna jaddada cewa ba za su bar farfajiyar gidan ba har sai an damke dan siyasar, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Original
Karin bayani na nan tafe...
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Asali: Legit.ng