Yadda minista Malami ya shiga, ya fita, ya nemi hana EFCC ta gurfanar da Okorocha

Yadda minista Malami ya shiga, ya fita, ya nemi hana EFCC ta gurfanar da Okorocha

  • Antoni-janar na tarayya kuma ministan shari'a ya umarci EFCC da ta dakata da tuhumar tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha
  • Sai dai a cewar Malami, tuhuma da binciken da EFCC take masa ya take hakkinsa na bil'adama, duba da yadda hukumar ta amshe masa fasfoti da sauran takardun tafiyarsa
  • Hakan yasa lauyan da ke karesa shigar da korafi, inda kotu ta umarci hukumar da ta sakar masa fasfotinsa da sauran takardun tafiyarsa amma EFCC tayi mirsisi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Antoni-janar na tarayya kuma ministan shari'a, Abubakar Malami, ya umarci hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC da ta dakata da tuhumar tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, wanda a baya hukumar ta yi ram da shi da karfi da yaji a ranar Talata, takardun da Premium Times ta gani ne suka bayyana hakan.

Kara karanta wannan

Harkallar Kwaya: Bayan tsallake kisa a magarkama, Kyari da abokansa sun bayyana a kotu

Umarnin da Malami ya bayar na dakatar da tuhumar yazo ne a wata wasikar da Abdulrasheed Bawa, shugaban EFCC ya fitar a ranar 21 ga watan Afirilu, a wani martani kan wasu korafe-korafe da Ola Olanioekun, lauyan Okorocha ya shigar.

Yadda minista Malami ya shiga, ya fita, ya nemi hana EFCC ta gurfanar da Okorocha
Yadda minista Malami ya shiga, ya fita, ya nemi hana EFCC ta gurfanar da Okorocha. Hoto daga thecable.ng
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kamar yadda wasikar da Malami ya sa hannu, Olanipekun, babban lauyan ya zargi EFCC da karya dokar kotu yayin tuhumar gami da kama tsohon gwamnan jihar Imo.

A korafin da Okorocha ya shigar, AGF ya janyoo hankalin EFCC a kan umarnin kotun da babbar kotun tarayya ta Port-Harcourt ta bayar, a shekarar da ta gaba yayin da hukumar.

Malami ya cigaba da cewa, bincike gami da tuhumar Okorocha ya ci karo da hakkinsa na damar sauraro yadda ya dace karkashin sashi na 6(6) a kundin tsarin shari'a na shekarar 1999.

Kara karanta wannan

Daga korafi a Facebook: Mutumin da gwamnan APC ya daure saboda sukar gwamnatinsa ya kubuta

A baya, an gano yadda EFCC da tawagar lauyoyin Okorocha suka dade suna dauki ba dadi a kan hukuncin kotun Port Harcourt.

Olanipekun, lauyan Okorocha ya shigar da korafi ga kotu, inda ya zargi EFCC da karya dokar kotu, wacce ta umarci hukumar da ta sakarwa sanatan fasfotinsa.

Bayan kin bin umarnin kotun da hukumar tayi, Okorocha ya sake shigar da kara a wannan dai kotun don tsare masa hakkinsa na bil'adama, wanda ya ce an take.

Olanipekun ya cigaba da shaida wa kotu duk da umarnin da ta bada, EFCC ta yi kunnen uwar shegu game da sakin fasfotin wanda ake karewa da sauran takardun tafiyarsa, inda ya kara da cewa, "Alamu na nuna yadda babu wata shari'a da aka yi a nan."

Sai dai lauyan EFCC, N A Dodo ya musanta karya dokar kotun da ake zargin EFCC tayi, inda ya ce hukumar ta kira Okorocha a waya tare da shaida masa ya zo ya amshi fasfotinsa da sauran takardun tafiyarsa, amma bai zo ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jami'an EFCC sun tasa keyar sanata Okorocha daga gidansa

Daga bisani hukumar ta damko shi da karfi da yaji a ranar Talata bayan daukar awanni 6 suna dakonsa a gidansa na Maitama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel