Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun halaka tsohon kwamishinan NPC, sun sace 'ya'yansa mata

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun halaka tsohon kwamishinan NPC, sun sace 'ya'yansa mata

  • Yan bindiga sun kutsa gidan tsohon kwamishinan NPC ta ƙasa, sun kashe shi kuma sun yi garkuwa da 'ya'yansa mata biyu
  • Rahoto ya nuna cewa maharan sun shiga gidan da tsakar dare, sun nemi a ba su miliyan N50m kuɗin fansa
  • Kakakin yan sandan jihar, ASP Ramhan Nansel, ya ce a halin yanzu jami'an tsaro sun bazama domin ceto waɗan da aka sace

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Nasarawa - Wasu miyagun yan bindiga sun kashe tsohon kwamishinan hukumar ƙidaya ta ƙasa (NPC), Zakari Umaru-Kigbu, a jihar Nasarawa, kuma suka sace ƴaƴansa mata biyu.

Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru bayan rabawar daren da ya gabata a gidansa da ke Azuba Bashayi, ƙaramar hukumar Lafiya jihar Nasarawa.

Haka nan kuma wasu bayanai sun nuna cewa maharan sun bukaci a tara musu miliyan N50m a matsayin kuɗin fansar waɗan da suka sace.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Wani ɗan majalisa tare da dandazon magoya bayansa sun fice daga NNPP ta Kwankwaso, sun koma APC

Yan bindiga sun kai hari Nasarawa.
Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun halaka tsohon kwamishinan NPC, sun sace 'ya'yansa mata Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ɗaya daga cikin iyalan gidan su marigayin, wanda ya nemi a ɓoye bayanansa, ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar a Lafiya, babban birnin Nasarawa, da safiyar Lahadi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Channels tv ta rahoto Ya ce:

"Yan bindiga sun kashe Umaru-Kigbu a cikin gidansa a daren da ya wuce a Azuba Bashayi, ƙaramar hukumar Lafiya, jihar Nasarawa kuma suka sace ƴaƴansa mata biyu."

Mamacin ɗan kimanin shekara 60 a duniya, tsohon jami'i ne a rundunar sojojin saman Najeriya.

Rahoto ya nuna cewa har zuwa lokacin da aka kashe shi, ya kasance lakcara a tsangayar koyar da aikin jarida a lsa Mustapha Agwai Polytechnic, Lafia (IMAP) kuma tsohon kwamishinan NPC na ƙasa da ke kula da Nasarawa.

Wane mataki hukumomin tsaro suka ɗauka?

Da yake tabbatar da lamarin, kakakin hukumar yan sandan Nasarawa, ASP Ramhan Nansel, ya ce rundunar yan sanda ta samu kiran gaggawa da ƙarfe 12:20 na ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Cikin Shauƙi: Hotunan kyakkyawar tarbar da aka yi wa shugaba Buhari da iyalansa a birnin Malabo

A cewarsa, yanzu haka jami'an yan sanda sun dukufa bincike don gano ainihin abin da ya faru har tsohon kwamishinan ya rasa rayuwarsu.

Nansel ya ƙara da tabbatar da cewa yan bindiga sun yi garkuwa da ƴaƴansa mata guda biyu a harin.

Kakakin yan sandan ya ce:

"Mun kai ɗauki ta hanyar tura jami'an tsaro masu Sintiri kuma an turo sojoji wurin da abun ya faru domin su taimaka a kuɓutar da 'ya'ya mata biyu ba tare da sun cutu ba."

Ya ƙara da cewa sun gaggauta kai Umaru-Kigbu zuwa Dalhatu Raf Specialist Hospital (DASH) da ke lafiya, inda anan ne rai ya yi halinsa.

A wani labarin na daban kuma Bayan janye takara, Sanatan APC ya sauya sheka daga jam'iyyar zuwa PDP

Sanatan Kebbi ta tsakiya kuma tsohon ministan Abuja, Sanata Adamu Aleiru ya suaya sheka daga APC zuwa jam'iyyar PDP.

Da farko dai Sanatan ya tsame kansa daga zaɓen fitar da ɗan takarar Sanatan APC, inda ya zargi cewa an shirya magudi da damfara.

Kara karanta wannan

An damke yaran siyasan Aisha Binani suna rabawa Deleget makudan kudi a Adamawa, Hotuna

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262