Hotunan kyakkywar tarbar da aka yi wa shugaba Buhari da iyalansa a Birnin Malabo

Hotunan kyakkywar tarbar da aka yi wa shugaba Buhari da iyalansa a Birnin Malabo

  • Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, tare da iyalansa sun samu kyakkyawar tarba yayin da suka isa birnin Malabo
  • A ranar Alhamis, shugaban tare da uwar gidansa, Aisha Buhari suka tafi ƙasar Equatorial Guinea, domin halartar wani taro
  • Buhari ya bar Najeriya ne yayin da jam'iyyarsa ke tsaka da gudanar da zaɓen fitar da yan takara a zaɓen da ke tafe

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

A ranar Alhamis, shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya fice daga Najeriya zuwa birnin Malabo na ƙasar Equatorial Guinea domin halartar taro na musamman na gamayyar shugabannin ƙasashen Afirka.

Taron dai na wannan lokacin da shugaba Buhari ya tafi, zai maida hankali musamman kan harkokin da suka shafi tsaro.

Shugaban ƙasan ya tafi ne bisa rakiyar uwar gidansa, Aisha Muhammadu Buhari da kuma wasu daga cikin 'ya'yansa mata.

Uwar gidan shugaban kasan ta tura kyawawan Hotunan tarbar da suka samu yayin da suka isa Birnin Malabo a Shafinta na Facebook.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Aisha Binani ta lallasa mazaje biyar, ta lashe zaben fidda gwanin APC a Yola

Aisha ta rubuta a shafinta cewa:

"Mun samu tarba mai kyau daga mai masaukin baki shugaban ƙasa, H.E, Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, da uwar gidansa, H.E, Constancia Mangue."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Duba Hotunan a nan ƙasa

Birnin Malabo
Hotunan kyakkywar tarbar da aka yi wa shugaba Buhari da iyalansa a Birnin Malabo Hoto: Aisha M Buhari/facebook
Asali: Facebook

Shugaba Buhati a Malabo
Hotunan kyakkywar tarbar da aka yi wa shugaba Buhari da iyalansa a Birnin Malabo Hoto: Aisha M Buhari/facebook
Asali: Facebook

Shugaba Buhari da iyalansa.
Hotunan kyakkywar tarbar da aka yi wa shugaba Buhari da iyalansa a Birnin Malabo Hoto: Aisha M Buhari/Facebook
Asali: Facebook

Shugaban ƙasa Buhari.
Hotunan kyakkywar tarbar da aka yi wa shugaba Buhari da iyalansa a Birnin Malabo Hoto: Aisha M Buhari/facebook
Asali: Facebook

Aisha Buhari a Malabo
Hotunan kyakkywar tarbar da aka yi wa shugaba Buhari da iyalansa a Birnin Malabo Hoto: Aisha M Buhari/Facebook
Asali: Facebook

A wani labarin na daban kuma Dr. Dikko Radda ya lashe zaben fidda gwanin APC a jihar Katsina

Tsohon darakta Janar na SMEDAN, Dr Dikko Umaru Radda, ya zama ɗan takarar gwamnan Katsina karkashin APC.

Radda ya samu tikitin APC ne bayan zama zakara a zaɓen fid da gwanin da ya gudana ranar Alhamis da kuri'u 506.

Asali: Legit.ng

Online view pixel