Yan sanda sun kama yan yankan aljihu 10 a wajen zaben fidda dan takarar shugaban kasa na PDP

Yan sanda sun kama yan yankan aljihu 10 a wajen zaben fidda dan takarar shugaban kasa na PDP

  • Jami'an yan sanda sun yi ram da wasu mutane 10 a wajen zaben fidda dan takarar shugaban kasa na PDP da aka yi a ranar Asabar
  • An kama mutanen ne kan zargin yiwa jama'a musamman deleget yankan aljihu tare da sace masu wayoyi
  • Wani jami’an dan sanda, Sufeto Maina Gambo ya bayyana cewa an kama yawancinsu ne a yayin da suke tsaka da aikata aika-aikar

Abuja - Rahotanni sun kawo cewa yan sanda sun damke wasu mutane 10 da ake zaton yan yankan aljihu ne a babban taron jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da aka yi a Abuja a ranar Asabar, 28 ga watan Mayu.

Wani jami’an dan sanda, Sufeto Maina Gambo ya fada ma kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a kofar ‘gate D’ na filin wasa na Moshood Abiola, cewa an kama yawancin wadanda ake zargin ne a yayin da suke tsaka da yankawa mutane aljihu.

Kara karanta wannan

Inyamurai ne: Gwamna ya bayyana masu hallaka mutane a yankin Kudu maso Gabas

Yan sanda sun kama yan yankan aljihu 10 a wajen zaben fidda dan takarar shugaban kasa na PDP
Yan sanda sun kama yan yankan aljihu 10 a wajen zaben fidda dan takarar shugaban kasa na PDP Hoto: Douye Diri
Asali: Facebook

Gambo ya ce:

“Ina ganin mun kama fiye da mutane 10 saboda ko a wannan kofar mun kama bakwai, yawancinsu an kama su ne suna satar wayoyin deleget.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Hakan kan faru ne a lokacin da mutane ke turereniyar shiga filin wasan.
“Akwai wani labara inda aka fizge agogon wani matashi sannan mutanen da ke wajen suka gaggauta sanar da lamarin sannan aka mika mana mai laifin.”

NAN ta kuma nakalto Gambo yana cewa an kwashi yawancin wadanda ake zargin zuwa ofishin yan sanda don bincike da hukunta su.

Ya kara da cewa:

“Muna da sashi na musamman da ke kula da irin wadannan lamura don tabbatar da cikakken bincike.”

Shugaban kasa a 2023: Atiku ya dauki wasu manyan alkawara, ya caccaki APC

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya dauki alkawarin hada kan kasar idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Zaben fidda gwanin PDP: DPO ya sha ruwan duwatse, an kashe wani a Gombe

Atiku ya kuma dauki alkawarin tunkarar matsalar rashin tsaro da ya addabi kasar nan, jaridar Punch ta rahoto.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake bayar da jawabin amincewarsa bayan an ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin shugaban kasa na PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng