Ku Bi Ƴan Ta'adda Inda Suke Ku Yaƙe Su, Ku Dena Jira Sai Sun Kawo Hari: Gwamnan Zamfara Ga Sojoji

Ku Bi Ƴan Ta'adda Inda Suke Ku Yaƙe Su, Ku Dena Jira Sai Sun Kawo Hari: Gwamnan Zamfara Ga Sojoji

  • Gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara ya bukaci sojojin Najeriya su bi ‘yan bindigan da su ka addabi mutanen jihar da yankin Arewa maso Yammacin kasar nan har maboyarsu don yakarsu
  • Ya ba su wannan umarnin ne yayin da ya amshe mambobin Kwalejin Yaki ta Sojojin Najeriya wadanda su ka kai masa ziyara a ranar Talata, inda ya ce kada su jira sai ‘yan bindigan sun kai farmaki
  • Ya ce sun fahimci cewa sojoji su na jin jiki saboda rashin tsaron da ke kasar nan, hakan ya sa su ka yanke shawarar sanya har sojoji masu murabus don kawo dauki

Zamfara - Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya bukaci rundunar sojin Najeriya ta fara kai wa ‘yan bindiga farmaki har maboyarsu sakamakon yadda su ka addabi jiharsa da yankin arewa maso yammacin kasar nan.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun saki sabon bidiyon fasinjojin jirgin Abuja-Kaduna, cikin har da dan kasar Pakistan

A ranar Talata Matawalle ya yi wannan maganar ne yayin da ya amshi mambobin Kwalejin Sojojin Najeriya ta Yaki wadanda su ka kai masa ziyara, Premium Times ta ruwaito.

Ku Bi Ƴan Ta'adda Inda Suke Ku Yaƙe Su, Ku Dena Jira Sai Sun Kawo Hari: Gwamnan Zamfara Ga Sojoji
Ku Bi Ƴan Ta'adda Mabiyarsu, Ku Dena Jira Sai Sun Kawo Hari: Gwamnan Zamfara Ga Sojoji. Hoto: Premium Times.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan ya ce wa sojojin su bi ‘yan bindiga don yakarsu maimakon su jira har sai sun kai wa jama’a farmaki kafin su mayar musu da hari.

Yayin da ya bayyana yadda sojoji su ke a takure kuma su na bukatar ababen yaki na zamani, Premium Times ta nuna inda ya ce su na sa ran za a karo makaman.

Matawalle ya ce Gwamnatin Tarayya ta na karo makaman zamani

Matawalle ya ci gaba da cewa:

“Mun fahimci cewa sojojin Najeriya su na fama sakamakon matsalolin tsaron da kasar nan ke fama da ita wacce yanzu haka duk wani jami’in tsaro ya shiga cikinta tsundum.”

Kara karanta wannan

Rayuwar dan Adam ta yi arha a Najeriya: CAN ta yi Alla-wadai da kisan Fatima da yaranta a Anambra

A matsayin hanyar taimaka wa ayyukan sojoji, gwamnan ya ce an sanya har jami’an soji masu murabus a cikin yaki da ta’addancin.

A cewarsa, gwamnatin tarayya ta yi kokarin ganin tana karo sabbin makaman yaki musamman don sojoji.

Kungiyar sojin ta ba Gwamna Matawalle lambar yabo

Shugaban kungiyar, wanda manjo janar ne, ya yaba wa Gwamna Matawalle akan kokarinsa wurin kara wa jami’an tsaro kwarin gwiwa.

Ya ce sojoji za su yi iyakar kokarinsu wurin kawo karshen ta’addanci a Najeriya.

Kungiyar ta bai wa gwamnan lambar yabo akan kokarinsa.

Zamfara, kamar sauran jihohin Najeriya na yankin arewa maso yamma, tana fama da farmaki iri-iri daga ‘yan bindiga wadanda su ka fi addabar ‘yan kauye da matafiya.

Ana kuka da ‘yan bindigan da yadda su ke halaka rayukan dubbanin jama’a a ko wacce rana.

Sun yi garkuwa da jama’a wadanda a tarihin Najeriya ba a taba samun matsalolin garkuwa da mutane ba kamar a wadannan ‘yan shekarun.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ga Najeriya: Ba zan huta ba har sai an samu zaman lafiya a kasar nan

'Yan Ta'addan Da Suka Kai Hari Sansanin Sojoji Na Kaduna Sun Ɗanɗana Kuɗarsu, Lai Mohammed

A bangare gudan, Gwamnatin Tarayya, a ranar Laraba ta ce yan ta'addan da suka kai hari sansanin sojoji da ke Birnin Gwari a Kaduna sun sha azaba a hannun sojoji a yayin da suka fatattake su, rahoton Daily Trust.

Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke amsa tambayoyi kan tsaro bayan taron FEC da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a Aso Villa a Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa sojoji 11 ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da wasu da dama suka jikkata yayin harin na ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164