Abba Kyari ya sha da kyar, saura kiris masu fushi da shi su hallaka shi a gidan yari

Abba Kyari ya sha da kyar, saura kiris masu fushi da shi su hallaka shi a gidan yari

  • Kimanin mutum 190 ne a gidan gyaran halin Kuje suka yi yunkurin halaka Abba Kyari sakamakon jikakkiyar da suke da ita yayin da yake aikin dan sanda
  • An gano cewa Abba Kyari ya karba wasu makuden kudade daga hannunsu a lokacin da ya ke aiki inda yayi musu alkawarin samar musu da kwangila
  • A halin yanzu an killace shi a gidan gyaran halin kuma ana tsananta tsaro a inda yake sannan ana tunanin mayar da shi hannun jami'an DSS
  • Bayanai daga majiyoyi masu karfi sun tabbatar da yadda ake barin Abba Kyari ya ga matarsa a duk lokacin da yaso kuma yake amfani da wayarsa duk da yana tsare

Kuje, Abuja - Jami'an gidan yari suna tunanin mayar da jami'in 'dan sanda Abba Kyari daga gidan yarin Kuje zuwa hannun jami'an tsarin farin kaya bayan wasu daga cikin abokan zamansa sun yi yunkurin halakasa sakamakon zarginsa da rashin gaskiya wajen bada cin hanci don a samar musu da kwangila a lokacin da yake kan aiki.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace malamin addini da wasu mutane 7 a jihar Katsina

Kamar yadda wasu takardun cikin gida da Premium Times ta samu damar gani suka bayyana, an kai masa harin ne a 4 ga watan Mayu, watanni bayan kama Kyari da laifin safarar miyagun kwayoyi. Maharansa sun kai kimanin 190, a cewar wani jami'i, kuma da yawansu an kai su gidan yarin ne saboda harkallar miyagun kwayoyi.

Abba Kyari ya sha da kyar, saura kiris masu fushi da shi su hallaka shi a gidan yari
Abba Kyari ya sha da kyar, saura kiris masu fushi da shi su hallaka shi a gidan yari. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Kyari, mai shekaru 47, mataimakin kwamishinan 'yan sanda, wanda jami'in tsaro ne sannan hazikin kungiyar binciken sirri na sifeta-janar kafin ya kwafsa.

Da farko dai an dakatar da shi daga aikin 'yan sanda bayan masu bincike na Amurka sun ambaci sunansa a matsayin mai hannu a sabgar damfara tsakanin kasa da kasa da sabgar damfarar Ramon Abbas wanda aka fi sani da Hushpuppi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A lokacin ne aka dakatar da shi, ana jiran sakamakon binciken cikin gida. Hukumar yaki da fasakwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA) a watan Fabrairu ta zarge shi da hannu a safarar miyagun kwayoyi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jami'an EFCC sun tasa keyar sanata Okorocha daga gidansa

Hukumar ta saki wani bidiyo, inda Kyari ya bayyana yana siffanta yadda tawagarsa ke harkallar safarar miyagun kwayoyi tare da tattaunawa a kan kasansu.

Yadda farmakin ya kasance

Maharan gidan yarin Kuje sun yi ikirarin Kyari ya yanke musu hukunci duk da yadda ya amshi cin hanci daga garesu, majiyoyinmu suka bayyana hakan.

Daya daga cikin majiyoyin, jami'in 'yan sandan farin kaya sannan jami'in binciken sirri, ya siffanta Kyari a matsayin "Kasurgumin 'dan ta'adda."

Har yanzu ba a yanke wa Kyari hukuncin wani laifi da ake tuhumarsa ba, kuma yaki amincewa da laifukan da ake tuhumarsa.

Majiyoyinmu yayin yanko maganar abokan zaman sa na gidan yari sun bayyana cewa Kyari na kokari wajen "Kawo karshen kananan masu safarar miyagun kwayoyi don taimakawa Adam Ukatu, wani biloniya da aka zarga da safarar miyagun kwayoyi na Tramadol na N3 biliyan wanda ke da Alaka da Kyari.

"Yayin da aka kama 'yan gidan yari da suka kai harin sun bayyana yadda Abba Kyari ya bukaci rashawa don kawo karshen lamarinsu, amma hakan bai tseratar da su daga gurfanar wa ba," wata majiya a gidan yarin Kuje wanda ya ji ta bakin maharan ya bayyana hakan.

Kara karanta wannan

Rundunar yan sanda ta tabbatar da kisan mutum 12 a wani harin sassafe da yan bindiga suka kai Katsina

Kakakin hukumar gidan gyaran halin, Francis Enobore, ya musanta harin da aka kai wa Kyari. Amma Premium Times ta tabbatar da hakan bayan daga jami'an da ke da masaniya a kan lamarin tare da samun takardun cikin gida.

Kamar yadda majiyoyinmu suka bayyana, jami'an tsaron gidan ne suka yi nasarar ceto Kyari, tun daga lokacin suka kebance shi a wuri na daban "tare da matsanancin kula inda babu mai ganin shi don gudun kada a sa mai guba."

"Don neman zaman lafiya, hakan yasa Kyari ya biya fusatattun 'yan gidan yarin N200,000 a farko sannan ya dauki nauyin biyan kudin Subscription na DSTV don a zauna lafiya," a cewar wata majiya.
Sai dai, Mr Enobore, kakakin gidan gyaran halin ya ce, "Bani da masaniya game da yadda Kyari ya biya wani kudI don neman zaman lafiya a gidan yari."

Duk da kudade da abubuwan tagomashin da ya basu, hakan bai sa sun janye yunkurin halakasa ba, a cewar majiyoyinmu.

Kara karanta wannan

Zaben fidda gwanin PDP: DPO ya sha ruwan duwatse, an kashe wani a Gombe

"Duk da irin tsaron da ake bashi, sun lashi takobin aikasa barzahu," a cewar wata majiya.
"'Yan gidan yarin sun bashi wani dan lokaci ya maido musu da duk abubuwan da ya amsa daga gare su ko kuma su halakasa.
"Manyan ma'aikatar sun tabbatar da cewa, akwai yuwuwar za a yi raunatasa ko ma a halakasa idan aka cigaba da barinsa a Kuje."

Wani jami'i ya bukaci a maida Kyari hannun hukumar farin kaya, Premium Times ta ruwaito.

Kakakin SSS, Peter Afunanya, bai amsa kiraye-kirayen waya ba, balle sakonnin da aka tura masa don jin ta bakin sa a kan lamarin.

Amma, majiyoyi daga gidan yarin Kuje sun siffanta rayuwar Kyari a gidan yarin da rayuwa mai cike da hatsari.

"A halin yanzu dai, yana da manyan jami'ai da yake basu ababen duniya. Suna bashi damar ganin matarsa, sannan yana anfani da wayarsa tare da ganin duk wanda yake so," a cewar wata majiyarmu.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda wani matashi ya yi bikin zagayowar ranar haihuwara a makabarta, mutane da dama sun halarci taron

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng