Yan bindiga sun sace malamin addini da wasu mutane 7 a jihar Katsina

Yan bindiga sun sace malamin addini da wasu mutane 7 a jihar Katsina

  • 'Yan bindiga sun yi awon gaba da wani limamin cocin katolika da wasu mutane bakwai a wani farmaki da suka kai garuruwan Katsina
  • An yi garkuwa da malamin addinin, mataimakinsa da wasu bakinsu biyu a kauyen Gidan Mai Kanbu da ke karamar hukumar Kafur ta jihar
  • Sannan a kauyen Bare-bari da ke karamar hukumar Safana, maharan sun yi garkuwa da mutane hudu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Katsina - Tsagerun yan bindiga sun yi garkuwa da wani limamin kotolika, Stephen Ojapa Ojapa, da mataimakinsa, Oliver Okpara, a kauyen Gidan Mai Kanbu da ke karamar hukumar Kafur ta jihar Katsina.

Majiyoyi a garuruwan Gozaki da Marabar Kanya sun bayyana cewa yan bindigar sun farmaki harabar cocin inda limaman cocin ke zama da safiyar yau Laraba, 25 ga watan Mayu, sannan suka yi awon gaba da shi da wasu bakinsu biyu, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Rundunar yan sanda ta tabbatar da kisan mutum 12 a wani harin sassafe da yan bindiga suka kai Katsina

Yan bindiga sun sace malamin addini da wasu mutane 7 a jihar Katsina
Yan bindiga sun sace malamin addini da wasu mutane 7 a jihar Katsina Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wani mazaunin Marabar Kanya, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce yan bindigar sun zo ne a kan babura, amma sai suka faka a nesa da wajen sannan suka taka da kafa zuwa cikin cocin.

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Mazauna Gidan Maikanbu sun bayyana cewa basu ji karar harbi a lokacin harin amma karar tashin babura da karfi da suka ji ya isa shaida. Bayan masu garkuwa da mutanen sun tafi ne wasu ma’aikatan cocin suka fara gudu don sanar da mutane batun harin."

Cocin Katolika ta Sokoto ta tabbatar da sace mutanen a cikin wata sanarwa ta yanar gizo mai dauke da sa hannun Daraktan labaranta, Chris Omotosho.

Sanarwar ta ce:

“Da tsakar daren yau, 25 ga watabn Mayu, 2022, yan bindiga sun farmaki cocin St. Patrick’s Catholic Church, Gidan Maikambo, karamar hukumar Kafur ta jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan Boko Haram sun yanka manoma 45 a wani sabon harin Borno

"An sace limamin cocin da mataimakinsa Rev. Frs. Stephen Ojapa, MSP, da Oliver Okpara da wasu yara biyu a gidan.
"Babu wani bayani game da inda suke. Ku yi masu addu'an tsira da kubuta. Nagode."

A wani labari makamancin haka, yan bindiga sun farmaki kauyen Bare-bari da ke karamar hukumar Safana inda suka sace mutum hudu.

Wani mazaunin kauyen Babban-dudu wanda ke kusa da garin da aka kai hari, ya ce shahararren dan siyasa a kauyen, Alhaji Dan Mashubulle, na cikin mutanen da aka sace a harin.

Ya kara da cewar harin ya shafe tsawon awanni yayin da yan bindigar suka bi gida-gida don sace dabbobi.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Gambo Isa, ya ce rundunar ba ta da masaniya game da sace mutanen amma za ta tuntubi DPO na karamar hukumar Kafur domin jin cikakken bayani, rahoton Daily Post.

Rundunar yan sanda ta tabbatar da kisan mutum 12 a wani harin sassafe da yan bindiga suka kai Katsina

Kara karanta wannan

Kuma dai: ‘Yan bindiga sun farmaki ofishin yan sanda a Anambra, sun kona motoci

A wani labarin, mun ji cewa tsagerun yan bindiga sun kashe akalla mutane 12 a kauyen Gakurdi da ke karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina, Channels TV ta rahoto.

Yan ta’addan sun kona gonaki da dama mallakar mazauna kauyen a yayin farmakin sassafe da suka kai yankin wanda ya shafe tsawon awanni.

Wani ganau ya shaidawa gidan talbijin na Channels cewa maharan dauke da muggan makamai sun isa kauyen ne a kan babura sannan suka fara harbi kan mai uwa da wabi don tarwatsa al’ummar garin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng