Da duminsa: 'Yan Boko Haram sun halaka 'yan sanda 2, sun raunata wasu 5 a Borno

Da duminsa: 'Yan Boko Haram sun halaka 'yan sanda 2, sun raunata wasu 5 a Borno

  • 'Yan sanda biyu sun sheka lahira yayin da wasu mutum biyar suka jigata sakamakon harin kwanton bauna da 'yan Boko Haram suka kai musu
  • An gano cewa, 'yan ta'addan sun lallaba ta kauyen Goni Matari da ke tsakanin Mainok da Jakan inda suka far wa 'yan sandan
  • Sun kone motoci biyu na sintirin 'yan sandan sannan suka cika bujensu da iska bayan sun hango jami'an sojin bataliya ta 29 da wasu 'yan sanda

Borno - A kalla 'yan sanda biyu sun rasa rayukansu yayin da waus mutum biyar suka samu miyagun raunika a lokacin da wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka kai harin kwanton bauna a kan babban titin Maiduguri zuwa Damaturu a jihar Borno ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

MNJTF sun bankado kasuwar ISWAP, sun damke 'yan ta'adda 30 a yankin tafkin Chadi

Wata majiyar tsaro ta sanar da Daily Trust cewa, 'yan ta'addan sun kai wa 'yan sandan hari ne a kauyen Goni Matari da ke tsakanain Mainok da Jakana a karamar hukumar Kaga ta jihar inda suka kone motocin sintiri biyu.

Da duminsa: 'Yan Boko Haram sun halaka 'yan sanda 2, sun raunata wasu 5 a Borno
Da duminsa: 'Yan Boko Haram sun halaka 'yan sanda 2, sun raunata wasu 5 a Borno
Asali: Original
"A sa'o'in farko na ranar Lahadi wurin karfe 8 na safe, 'yan ta'addan Boko Haram sun kai wa 'yan sandanmu harin kwanton bauna. Sun ajiye ababen hawansu inda suka lallaba suka shiga ta wurin kauyen Goni Matari, wanda shi ne hanyar tsallakewa.
"Sun kara da kone ababen hawa biyu na 'yan sandan wadanda ake sintiri da su sannan suka tsere bayan sun hango jami'ai karkashin jagorancin kwamandan bataliya ta 29 tare da 'yan sandan rundunar CRACK da na RRS.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Tawagar 'yan sandan da aka turo daga ofishinsu na Borno ne suka dauka gawawwakin 'yan sandan biyu," majiyar tsaron ta ce.

Kara karanta wannan

Borno: Jirgin NAF ya yi amon wuta kan tawagar Boko Haram/ISWAP, 'yan ta'addan sun salwanta

MNJTF sun bankado kasuwar ISWAP, sun damke 'yan ta'adda 30 a yankin tafkin Chadi

A wani labari na daban, jami'an rundunar hadin guiwa ta kasashe, MNJTF sun bankado kasuwar kifi ta Boko Haram a yankin tafkin Chadi kuma sun kama mutane 30 da suka yi ikirarin cewa su masunta ne da manoma, majiyar tsaro ta tabbatar.

An gano cewa kasuwar ce babban jigon samun kudi ga 'yan ta'addan wanda suke amfani da shi wurin siyan makamai da harsasai.

"Dakarun sun gano kasuwar kifi a wani babban sintirin da suka je Tamfalla, fitacciyar kasuwar kifi da ke karamar hukumar Kukawa," wata majiya tace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel