Za mu sha farfesu: 'Yan Najeriya sun bar jama'a cikin mamaki bayan kamo kifin N500k a teku

Za mu sha farfesu: 'Yan Najeriya sun bar jama'a cikin mamaki bayan kamo kifin N500k a teku

  • Wasu mutane uku sun kama wani kifi mafi sauri a duniya a tekun Legas wanda kudinsa ya kai sama da N500k
  • Daya daga cikin mutanen, wanda injiniyan ruwa ne ya shaida ma majiyar Legit.ng cewa, sun dana tarkon kama kifin ne da wasa kuma ba su yi tsammanin za su iya kama shi ba
  • Ya ce yanzu haka sun ajiye babban kifi a cikin injin daskarer da abinci kuma za su iya cinye shi idan ba a zo saye ba

Legas - Wani injiniyan ruwa mai suna Pakama da wasu abokan aikinsa biyu sun yi amfani da shafin Twitter don nuna babban kifin da suka kama a tekun da ke unguwar anchorage na jihar Legas.

Pakama ya yada hotunansa da abokan aikin nasa suna tare da babban kifin ya kuma rubuta: "Mun kama kifin yin farfesu."

Kara karanta wannan

Ina tsananin bukatar aure cikin gaggawa, Wata Jarumar masana'antar Fim a Najeriya ta cire kunya

Yadda wasu suka kamo kifin farfesu
Za su iya cinyewa: 'Yan Najeriya bar jama'a cikin mamaki bayan kamo kifi mai darajar N500k | Hoto: @Mista_YPNation
Asali: UGC

Mutanen ba su taba tsammanin kama kifi mafi sauri a duniya ba

Pakama mai shekaru 32 ya shaidawa wakilin Legit.ng, Victor Duru cewa sun kama kifin ne a ranar Talata, 25 ga watan Mayu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Injiniya mai cike da farin ciki ya ce abokan aikinsa guda biyu sun kafa tarkon kifin da wasa a yammacin ranar Litinin kuma ba su taba tsammanin za su iya kama irin wannan kifin ba.

A cewarsa:

"Abokan aiki na biyu sun dasa kugiya tare da karamin kifi a matsayin fatsa a yammacin da ta gabata kuma gaskiya sun yi hakan cikin wasa ne ba tare da tsammanin kamu mai girma ba."

Pakama ya ce yayin da yake gudanar da zagayen da ya saba yi a wannan safiya mai cike da sa'a, ya lura da kifin da ke fatsal-fatsal wanda daga nan ya sanar da abokan aikinsa.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ga Najeriya: Ba zan huta ba har sai an samu zaman lafiya a kasar nan

Da aka tambaye su kan abin da za su yi da kifin, Pakama ya ce za su iya ci idan ba wanda ya zo ya saya.

A cewar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa, kifin da ya zo daga tekun pacific (mai girman inci 100) ya kai akalla $1,400 (N581k) kuma ya kan kai $1,520 (N639k) idan ya kai girman inci 110. Shi ne kifi mafi sauri a duniya.

Martanin 'yan Twitter

@dhotun ya ce:

"Kada kowa yayi maka karya.
“Rayuwar kan teku tana cike ne da kalubale.
"Lokacin da za ku kama kifi kamar marlin ko wani babban kifi mai ban sha'awa ne kadai abin sha'awa. Don haka ku ji dadinku! Wasu suna zaman teku na watanni 6-9 a cikin jirgin. Ku cinye kifinku ko ya daraja $10m."

@Chi_oma3 ya ce:

“Idan a Najeriya ne za a iya kama kifin kuma babu abin da zai faru sai dai a kasashen waje suna da ka’idoji na irin kifi da ya kamata a kama da kuma dalilai masu inganci.

Kara karanta wannan

Amma dai tela bai kyauta ba: Dinkin rigar wani yaro ya girgiza intanet, ana ta cece-kuce

"Bai kamata mu gama da nau'in ababen tekunmu ba saboda muna so mu ci farfesu. Wannan kifi yana da kyau."

@adeniyi____ ya ce:

"Fararen mutane za su kama kifi, kawai a dauki hotuna da shi a sake mayar da shi cikin ruwa, wasu daga cikin kifin nan da yawa ba su da yawa kuma suna gab da karewa. Ku daina cin su don Allah, akwai nau'ikan kote da Titus a kasuwa idan kuna son ci."

Wani mutumi dan Najeriya ya kama wata irin kifi yayin gina rami a Yenagoa

A wani labarin, a cikin wani sakon da ya riga ya yadu a kafofin watsa labarun, wani saurayi ya bayyana yadda ya sami wata kifi mai ban mamaki yayin da yake gina rami a Yenagoa, Jihar Bayelsa.

Wani mutum na Najeriya ya sa mutane cikin mamaki a kan wata hoto da ya yada a kafofin watsa labarai na kifin da ya gino daga wani rami.

Kara karanta wannan

Duniya kenan: An kama wasu mutane dan suka hallaka yaro da shekara 4 da sunan tsafi

A cewar wani sakonshi a shafin sa na Facebook, Emmanuel Emmanuel Udoh, yana yin aikinsa na gine-gine a lokacin da ya ga kifin da ya kamata yana cikin ruwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel