Katsina Ba Ta Siyarwa Ba Ce, Ɗalibai Ga Wakilan Jam'iyyu

Katsina Ba Ta Siyarwa Ba Ce, Ɗalibai Ga Wakilan Jam'iyyu

  • Kungiyar Hadin Kan Daliban Jihar Katsina, a jiya ta yi zanga-zangar lumana inda ta yi kira ga wakilan manyan jam’iyyu
  • A zanga-zangar ta yi kira ga wakilan akan su zabi ‘yan takarar gwamna na kwarai wadanda za su gina jihar su kuma kawo ci gaba
  • Daliban sun dinga zagayen duk wasu manyan titinan da ke cikin garin Katsina da takardu wadanda su ka rubuta 'Jihar Katsina ba ta siyarwa ba ce'

Katsina - A jiya ne Kungiyar Hadin Kan Daliban Jihar Katsina ta shirya zanga-zangar lumana musamman ga wakilan manyan jam’iyyu akan su zabi ‘yan takarar gwamna na kwarai wadanda za su ciyar da jihar gaba.

Daily Trust ta ruwaito cewa daliban sun dinga zagaye manyan titinan da ke garin Katsina rike da takardu wadanda su ka rubuta, “Jihar Katsina ba ta siyarwa ba ce”.

Kara karanta wannan

Ko anini ba zan ba da ba: Shehu Sani ya ce ba dashi ba biyan deliget a zaben fidda gwani

Katsina Ba Ta Siyarwa Ba Ce, Ɗalibai Ga Wakilan Jam'iyyu
Katsina Ba Ta Siyarwa Ba Ce, Ɗalibai Suka Fada Wa Wakilan Jam'iyyu. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yayin zantawa da manema labarai, shugaban daliban, Aliyu Mamman, ya nemi wakilan su duba zabin da ke zuciyoyin mutanen jihar wadanda su ka zarce mutane miliyan takwas a zuciyarsu.

Ya ce su zabi shugabannin da za su tallafawa jihar

A cewarsa bisa ruwayar Daily Trust:

“Mun samu labarin yadda ‘yan takarar su ke ta shaka wa wakilan jam’iyyu kudade masu tarin yawa don zabensu a zaben fidda-gwani.
“Don haka yayin amsar kudin, su tuna da mutanen Jihar Katsina wadanda su ka zarce mutane miliyan takwas wadanda duk sun dogara da su.
“Su ji tsoron Ubangiji kuma su zabi ‘yan takarar da su ka dace masu son jama’a, kuma wadanda za su yi wa al’umma aiki.”

Mamman ya ci gaba da cewa su na son wakilai su zabi shugabannin da za su kawo karshen kalubalen da jihar ke fustanta kuma su kara da wasu ayyukan.

Kara karanta wannan

Rikicin gidan PDP ya jagwalgwale a Kano, an rasa gane wadanda za su yi takara a 2023

2023: Tsohuwar Matar Shugaban APC Na Kasa Ta Siya Fom Din Takarar Gwamna a Nasarawa

A wani rahoton, Fatima Abdullahi, tsohuwar matar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, ta siya fom din takarar gwamnan Jihar Nasarawa, The Sun ta rahoto.

Za ta tsaya takarar ne don a yi zaben fidda gwani na jihar nan da wata daya, The Punch ta ruwaito.

Yayin da ta ke bayani bayan tuntubar shugabannin APC a ofishin jam’iyyar da ke Lafia, ranar Juma’a, Fatima ta ce ta tsaya takarar ne don gyara akan kura-kuran da wannan mulkin ya yi.

A cewarta, Jihar Nasarawa tana bukatar shugaba mai hangen nesa da kuma jajircewa don ciyar da jihar gaba.

Saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164