An gudu ba'a tsira ba: An bankado wani sirrin cin hanci na sabon Akanta Janar da Buhari ya nada
- Rahoto ya nuna cewa sabon mukaddashin Akanta Janar na kasa da Buhari ya nada, Anamekwe Nwabuoku, na karkashin bincike a hukumar EFCC
- Akwai tarin zarge-zarge a kan Nwabuoku ciki harda wawure kudaden da aka warewa bangaren tsaron cikin gida a lokacin da yake matsayin daraktan kudi a Ma’aikatar tsaro
- Har ila yau, daga cikin zargin da ke kansa harda na yin kutse a tsarin GIFMIS wajen satar albashin ma’aikatan gwamnatin tarayya
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Sabon mukaddashin Akanta Janar na kasa da aka nada, Anamekwe Nwabuoku, yana da zarge-zarge a kansa na rashawa kuma yana karkashin binciken hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Daily Nigerian ta rahoto.
Ku tuna cewa a ranar Lahadi da ya gabata ne aka nada Mista Nwabuoku domin ya jagoranci ofishin Akanta Janar din bayan da aka dakatar da Ahmed Idris, wanda ke hannun EFCC kan zargin wawure kudi har naira biliyan 80.
Sai dai kuma wani rahoton Economic Confidential ya yi ikirarin cewa sabon mukaddashin AGF din na da tarin zarge-zarge na rashawa a kansa.
Rahoton ya kara da cewa daga cikin zarge-zargen da ke kansa harda na biyan kansa makudan kudade a ma’aikatun da ya yi aiki a baya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar ta tattaro cewa hukumomin yaki da rashawa sun kwato wasu daga cikin kadarorin da ya mallaka ta hanyar sata.
Wata majiya ta sanar da jaridar cewa babban laifin da ya aikata shi ne yadda ya dungi satar kudade a lokacin da yake matsayin daraktan kudade da asusun a ma’aikatar tsaro ta kasa, inda ya azurta kansa da kudaden tsaron cikin gida.
An kuma tattaro cewa ya aikata almundanar kudade da dama tare da amfani da tsarin GIFMIS wajen satar albashin ma’aikatan gwamnatin tarayya.
GIFMIS wani tsari ne na sarrafa kasafin kudi da lissafin kudi. Gwamnatin tarayya ta fara amfani da shi ne duk a cikin dabarun sake fasalin ayyukan gwamnati tun a farkon shekarar 2000.
Mista Neabuoku ya yi kutse cikin tsarin sannan ya wawure makudan kudade.
Da aka nemi ya yi bayanin dalilin da yasa gwamnatin tarayya ta zabi nada mutumin da ke da wannan tarin badakaloli don jagorantar kujerar AGF, wani babban jami’in fadar shugaban kasa ya ce Mista Neabuoku ne mai babban matsayi a ofishin.
Jami’in ya ce:
“Ba rikon kwarya yake yi a matsayin AGF ba illa yana kula da harkokin ofishin ne a matsayinsa na babban darakta a ofishin.”
Saura yan watanni kadan Mista Neabuoku ya kai shekarun ritaya daga aikin gwamnati.
Buhari ya nada sabon mukaddashi Akanta Janar, ya maye gurbin Ahmed Idris dake hannun EFCC
A baya mun ji cewa Gwamnatin tarayya ta nada Mr Anamekwe Nwabuoku matsayin sabon mukaddashin Akanta Janar na tarayya.
Sakataren din-din-din ma'aikatar kudi, kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, Aliyu Ahmed, ya bayyana hakan a wasikan da ya ake ranar 20 ga Mayu, 2022.
An nada Nwabuoku ya haye kujeran Ahmed Idris da akewa zargin almundahanar N80bn.
Asali: Legit.ng