Yanzu-yanzu: Buhari ya nada sabon mukaddashi Akanta Janar, ya maye gurbin Ahmed Idris dake hannun EFCC

Yanzu-yanzu: Buhari ya nada sabon mukaddashi Akanta Janar, ya maye gurbin Ahmed Idris dake hannun EFCC

  • Mako daya da dakatad da Ahmad Aliyu, Ministar kudi ta nada sabon mukaddashin Akanta janar na tarayya
  • Gwamnatin tarayya na zargin Ahmed Idris da handamar sama da naira bilyan tamanin na al'umma
  • Rahotanni na nuna cewa sabon wanda aka nada shima hukumar EFCC na gidanar da bincike kansa

Abuja - Gwamnatin tarayya ta nada Mr Anamekwe Nwabuoku matsayin sabon mukaddashin Akanta Janar na tarayya.

Sakataren din-din-din ma'aikatar kudi, kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, Aliyu Ahmed, ya bayyana hakan a wasikan da ya ake ranar 20 ga Mayu, 2022.

An nada Nwabuoku ya haye kujeran Ahmed Idris da akewa zargin almundahanar N80bn.

Yanzu-yanzu: Buhari ya nada sabon mukaddashi Akanta Janar, ya maye gurbin Ahmed Idris dake hannun EFCC
Yanzu-yanzu: Buhari ya nada sabon mukaddashi Akanta Janar, ya maye gurbin Ahmed Idris dake hannun EFCC
Asali: Original

Bayan gano gidajensa 17 a gida da waje, kotu ta baiwa EFCC daman cigaba da rike Akanta Janar

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Kala-Balge: Zulum ya kai ziyarar jaje ga iyalan mutane 30 da aka yanka a Borno

EFCC ta samu izinin kotu don cigaba da rike Akanta Janar na tarayya, Ahmed Idris.

Wani jami'in hukumar wanda aka sakaye sunansa ya bayyana cewa hukumar ta samu izinin ne cikin kwana 1 da kama shi, rahoton Daily Trust.

Ya ce an basu daman su cigaba da tsareshi har sai an kammala bincikensa.

Yayinda aka tambayesa yaushe za'a sake shi, jami'in yace ai nan ba da dadewa ba za'a gurfanar da Ahmed Idris gaban kotu saboda hujjojin da aka samu kansa na da ban tsoro.

An gano gidajensa guda 17 a Landan, Abuja, Legas, Kano da Dubai

EFCC ta bankado gidajen Akanta Janar na tarayya, Ahmad Idrs, guda goma sha bakwai (17).

Punch ta ruwaito cewa wani jami'in EFCC wanda ya bukaci a sakaye sunansa yace Idris ya mallaki gidaje a Kano, Lagos, Abuja, Dubai da London

Ya kara da cewa an gani Ahmad Idris ya yi amfani da wasu makusantarsa wajen sayen wadannan dukiyoyi.

Kara karanta wannan

EFCC ta gano sabbin N90bn da AGF Ahmed Idris ya wawure, ya tona asirin minista da wasu jiga-jigan gwamnati

A cewarsa da yiwuwan ya sadaukarwa gwamnati wadannan gidaje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel