Neja: 'Yan Sanda Sun Kama Wani, Lawan Abubakar, Kan Yunƙurin Tono Gawa a Maƙabarta

Neja: 'Yan Sanda Sun Kama Wani, Lawan Abubakar, Kan Yunƙurin Tono Gawa a Maƙabarta

  • Rundunar ‘yan sandan Jihar Neja ta ce ta kama wani Lawal Abubakar mai shekaru 16 yayin da ya ke yunkurin tono gawa a makabartar Chanchanga
  • Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun ya bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai a ranar Litinin a Minna
  • Abiodun ya ce bayan sun titsiye matashin ya shaidar cewa sun hada kai da wani Hamisu ne don su samu sassan jikin gawar da sutturarta

Neja - Rundunar ‘yan sandan Jihar Neja ta yi ram da Lawal Abubakar, dan shekara 16, wanda mazaunin Kasuwan-Gwari ne da ke cikin Minna, inda su ke zarginsa da yunkurin tono wata gawa daga kabarinta a makabartar Chanchaga.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa a ranar Litinin, DSP Wasiu Abiodun ya bayyana hakan a wata tattaunawa da su ka yi da wakilin NAN a Minna.

Kara karanta wannan

An shiga rudani, wasu sun 'sace' masu kada kuri’a wajen zaben tsaida ‘Yan takaran PDP

Neja: 'Yan Sanda Sun Kama Wani, Lawan Abubakar, Kan Yunƙurin Tono Gawa a Maƙabarta
'Yan Sandan Nejja Sun Kama Wani, Lawan Abubakar, Kan Yunƙurin Tono Gawa a Maƙabarta. Hoto: The Punch.
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda ya shaida:

“Da misalin karfe 10:20 na safiyar Asabar, jami’an ‘yan sanda na ofishin Chanchaga su ka kama wani Lawali Abubakar, mazaunin Kasuwan-Gwari da ke Minna.
“An kama shi ne a makabartar Chanchaga inda ake zarginsa da yunkurin tono wata gawa daga kabarinta.”

Abiodun ya ce ana ci gaba da bincike

A cewar Abiodun, yayin da aka tasa shi gaba da tambayoyi, ya bayyana cewa ya hada kai da wani Hamisu ne don su samo sassan jikin gawa da kuma sutturarta a makabartar.

Ya ce yanzu haka ana kan bincike akan lamarin kuma ana ci gaba da neman Hamisu, rahoton Daily Trust.

Abiodun ya shaida cewa za a yanke musu hukuncin da ya yi daidai da abinda su ka aikata da zarar bincike ya kammala.

Wani mutum ya gamu da ajalinsa yayin da ya shiga maƙabartar musulmi cikin dare don haƙo gawa

Kara karanta wannan

Zagin Annabi: Ƴan Sanda Sun Tabbatar An Ƙona Gidaje 6 Da Shaguna 7 a Bauchi

A wani labarin daban, wani mutum da ba a gano ko wanene ba ya mutu yayin da ya ke yunkurin hako gawa a makabarta da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, Premium Times ta ruwaito.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a makabartar musulmi da ke Iberekodo, karamar hukumar Abeokuta ta Arewa na jihar Ogun.

Abimbola Oyeyemi, mai magana da yawun yan sandan jihar Ogun, ya tabbatarwa Premium Times afkuwar lamarin a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel