Wani mutum ya gamu da ajalinsa yayin da ya shiga maƙabartar musulmi cikin dare don haƙo gawa

Wani mutum ya gamu da ajalinsa yayin da ya shiga maƙabartar musulmi cikin dare don haƙo gawa

  • Mutanen garin Iberekodo sun farka sun tsinci gawar wani mutum a cikin makabartar musulmi
  • Wasu mazauna Iberekodo suna tunanin gawar ne ta kashe mutumin da aka tsinci kayan haki a kusa da gawarsa
  • Kakakin yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce ana zurfafa bincike

Abeokuta, Ogun - Wani mutum da ba a gano ko wanene ba ya mutu yayin da ya ke yunkurin hako gawa a makabarta da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, Premium Times ta ruwaito.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a makabartar musulmi da ke Iberekodo, karamar hukumar Abeokuta ta Arewa na jihar Ogun.

Wani mutum ya gamu da ajalinsa yayin da ya shiga maƙabartar musulmi cikin dare don haƙo gawa
'Yan sandan Nigeria. Hoto: Premium Times

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun far ma matafiya, sun yi garkuwa da mutum 5 a Ondo

Abimbola Oyeyemi, mai magana da yawun yan sandan jihar Ogun, ya tabbatarwa Premium Times afkuwar lamarin a ranar Laraba.

Amma ya ce ba zai iya tabbatar da abin da ya kashe mutumin ba, ya kara da cewa an kai gawar mutumin dakin ajiye gawa na Abeokuta.

Ya ce:

"Eh, an tsinci gawa a makabartar musulmi da ke kusa da Iberekodo. An tafi da gawar dakin ajiye gawa an fara bincike."

Abin da wasu mutanen garin suka ce game da lamarin?

Muheed Adeniyi, wani shaida, ya ce an tsinci gawar mutumin ne a cikin makabartar a safiyar ranar Lahadi.

A cewarsa, an tsinci gawar mutumin ne kusa da wata kabari da ya riga ya haka domin ciro gawar da ke ciki.

Adeniyi ya ce:

"Babu wanda ya san abin da ya kashe mutumin. Mun ga kayan haka rami a wurin. Ba mu san abin da ya kashe shi ba. Wata kila gawar ne ta kashe shi."

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Bidiyo ya bayyana yayin da Sheikh Gumi ya ziyarci mahaifar Sunday Igboho

Mazauna yankin sun ce mutumin ya mutu, wasu na ganin fatalwar gawar ce ta kashe shi.

Sheikh Gumi ya faɗawa Fulani yadda za su yi wa kansu gata a Nigeria

A wani labarin daban, Malamin addinin musulunci mazaunin Kaduna, Dr Ahmad Gumi, ya yi kira ga fulani a su tabbatar sun yi rajista sun kuma karbi katin zabe gabanin babban zaben 2023 da ke tafe a kasar, Daily Trust ta ruwaito.

A cewarsa, samun katin zaben yana da muhimmanci domin hakan zai basu damar zaben shugabanni da za su yi jagoranci na gari sannan su kare musu hakkokinsu.

Gumi ya ce akwai bukatar Fulani su yi rajistan kamar sauran yan Nigeria, domin su zabi mutanen da za su kiyayye musu dabobinsu da dukiyoyinsu da rayukansu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel