Yanzu-yanzu: Mataimakin Sifeton yan sanda, AIG Don Awunah, ya mutu

Yanzu-yanzu: Mataimakin Sifeton yan sanda, AIG Don Awunah, ya mutu

  • Cikin shekarar nan kadai, wani babban jami'in hukumar yan sanda ya sake mutuwa a asibiti a birnin tarayya Abuja
  • Wannan ya biyo bayan mutuwar DIG Egbunike wanda ya mutu kwanakin baya bayan cikin Kifi

Abuja - Mataimakin Sifeton yan sandan Najeriya, AIG Don Awunah, ya rigamu gidan gaskiya.

The Nation ta ruwaito cewa AIG Don Awunah ya mutu ne da safiyar Litinin bayan gajeruwar jinya da yayi a wani asibiti dake birnin tarayya Abuja.

Kakakin hukumar yan sanda jihar, CSP Olumiyiwa Adejobi, ya tabbatar da mutuwarsa.

Yanzu-yanzu: Mataimakin Sifeton yan sanda, AIG Don Awunah, ya mutu
Yanzu-yanzu: Mataimakin Sifeton yan sanda, AIG Don Awunah, ya mutu
Asali: Original

IGP na ya sanda ya jinjinawa Sajen Yahaya da ya ki amsan cin hancin N300,000

A wani labarin, Sifeto Janar na yan sanda, IGP Baba Alkali, ya jinjinawa wasu jami'an yan sanda biyu da suka nuna kwarewa wajen aikinsu ta hanyar fin karfin zukatarsu kan kudi.

Kara karanta wannan

Innalillahi: ‘Yan bindiga sun bindige tsohon kwamishina, sun sace ‘ya’yansa mata

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

IGP ya ce ya kamata a rika yabawa yan sanda irin wadannan da suka ki bin son zuciyarsu tare da gyara sunan hukumar.

Shugaban yan sandan ya jinjinawa Sergeant Yahaya Ahmed wanda wani Chukwuka Jude ya baiwa cin hancin naira dubu dari uku amma yaki amsa.

Hakazalika wani jami'i Samson Ekikrere wanda ya kwato jakar kudin wani kuma ya mayar masa da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel