Matasan Musulmai sun fito neman matar da ta zagi Annabi ruwa a jallo a Bauchi, an harbe mutum 2
- Fusatattun matasa a jihar Bauchi sun bazama neman matar da ta taba mutuncin Annabi Muhammad
- Sai dai matasan sun farma wasu kiristoci tare da lalata kayayyaki mallakarsu sakamakon rashin ganin matar wacce tuni aka boye ta
- A halin da ake ciki, rundunar yan sandan jihar ta bayyana cewa jami'anta sun yi nasarar kwantar da tarzoman, sun kuma ce tuni zaman lafiya ya dawo yankin
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Bauchi - Jama’a sun shiga tashin hankali a Bauchi kan zargin zagin Annabi da wata ma’aikaciyar kiwon lafiya ta jihar Bauchi, Roda Jatau ta yi, inda ta tura wani bidiyon cin mutuncin Annabi zuwa shafin Whatsapp, rahoton The Nation.
An tattaro cewa matasa Musulmai sun bazama neman matar wacce ta kasance yar asalin jihar Gombe amma take aure a yankin Warji da ke jihar, jim kadan bayan sallar Juma’a, amma basu same ta ba saboda an gudun da ita zuwa wani waje.
Hakan ya tunzura fusatattun matasan inda suka lalata kayayyaki mallakar kiristoci a yankin sannan suka cinnawa gidajensu wuta.
Sunday Vanguard ta tattaro cewa matasan sun jiwa wasu kiristoci rauni ciki harda wani faston Ecwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A halin yanzu, zaman lafiya ya dawo yankin bayan an tura rundunar yan sanda masu kwantar da tarzoma.
Wata sanarwa daga rundunar yan sandan jihar ta ce:
“Tuni aka tura tawagar tsaro ta yan sanda da masu kwantar da tarzoma wadanda kokarinsu ya daidaita lamarin. A yanzu hankula sun kwanta a yankin, yayin da ake gudanar da sintiri domin wanzar da zaman lafiya.”
Rundunar ta roki jama’a da su kantar da hankulansu sannan su gudanar da harkokinsu ba tare da tsoron fuskantar barazana ba domin zaman lafiya ya dawo yankin da abun ya shafa.
Batanci ga Annabi: Gwamnati ta cire takunkumi a Sokoto, ta haramta zanga-zanga
A wani labarin, gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, a ranar Juma'a, ya dage dokar hana fita da aka kafa a birnin Sokoto, sakamakon rikicin da ya biyo bayan kisan Deborah Samuel.
Gwamnan ya kuma haramta duk wani nau'in zanga-zanga da gangami a fadin a jihar har sai baba-ta-gani, Channels Tv ta ruwaito.
Rahotanni a baya sun ce, wasu fusatattu sun lallasa Deborah Samuel, dalibar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari, bisa zarginta da dura ashariya ga manzon Allah SAW.
Asali: Legit.ng