Jarumar Kannywood Daso ta shiga tseren neman kujerar sanata a Kano

Jarumar Kannywood Daso ta shiga tseren neman kujerar sanata a Kano

  • Jarumar fim Saratu Gidado ta ayyana aniyarta ta son takarar kujerar sanata a babban zaben 2023 mai zuwa
  • Saratu wacce aka fi sani da Daso ta ce za ta yi takarar ne domin ceto kasar daga mawuyacin halin da take ciki a yanzu haka
  • Sai dai kuma, shahararriyar jarumar ta Kannywood ta ce za ta sanar da jam'iyyar da za ta yi takara a ciki nan gaba kadan

Kano - Shahararriyar jarumar Kannywood, Saratu Gidado wacce aka fi sani da Daso, ta bayyana kudirinta na son takarar kujerar sanata a zaben 2023 mai zuwa.

Daso a wata wallafa da ta yi a shafinta na Instagram dauke da fostarta, ta bayyana cewa za ta nemi kujerar ne a mahaifarta ta jihar Kano, amma bata sanar da a kowani yanki bane za ta yi takarar.

Kara karanta wannan

Saraki ya bayyana ainahin abun da ya haddasa rashin tsaro a Najeriya

Sai dai ta kuma bayyana cewa nan ba da dadewa ba za ta sanar da jam’iyyar da a karkashin inuwarta za ta yi takara, inda ta bukaci mutane da su taya ta da addu’a.

Jarumar Kannywood Daso ta shiga tseren neman kujerar sanata a Kano
Jarumar Kannywood Daso ta shiga tseren neman kujerar sanata a Kano Hoto: saratudaso
Asali: Instagram

Ta rubuta a shafin nata:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“#siyasa Barka da safiya ya yan uwana yan Najeriya sannan ina maku barka da karshen mako.
“Ina burin sanar da abin da kezuciyata da kuma sanar da ku cewa zany i takarar kujerar sanata a jihata ta Kano. Nan ba da dadewa b azan sanar da jam’iyyar.
“Ina barar addu’arku ce kawai.
“Manufar: Don ceto kasar daga mawuyacin halin da take ciki. Nagode.”

Jama'a sun yi martani kan haka:

abbaelmustapha1 ya yi martani:

“Ki dauka da muhimmanci dan Allah. Za ki iya cimma hakan.”

sadiya.umar_ibrahim ta ce:

"Wayyo Allah cikina mama"

borno_gidankanshi ta yi martani:

Kara karanta wannan

2023: Maza sun gaza, cikin wata 6 mata da matasa za mu gyara Najeriya, 'Yar takarar APC

"Allah ya zaabah Miki Mafi Alheri "

dr_tafida y ace:

“ALLAH bada Sa’aa mama .”

last_done_backup ya ce:

“HAJIYA MAMA DASO ALLAH Y IDDA NUFI.
“Allah y taya riko”

Jarumin Kannywood, Ali Rabiu Ali, ya fito takarar ɗan majalisar tarayya a 2023

A gefe guda, mun ji a baya cewa jarumi a masana'antar shirya fina-finan Hausa Kannywood, Ali Rabiu Ali, ya tsaya takarar ɗan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar mazaɓar Dala ta jihar Kano.

A wata Fasta da jarumin ya saki a shafinsa na Instagram, Ali wanda aka fi sani da Daddy ya nuna cewa yana fatan ya zama magajin Malam Aminu Kano.

Ali wanda Furudusa ne kuma Darakta a Kannywood a ya wallafa Hotonsa ɗauke da Fom ɗin takara karkashin inuwar jam'iyyar PRP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel