Ci gaba ga kere-kere: An kere Keke-Napep na farko a Najeriya, an fantsama kasuwa
- 'Yan Najeriya na ci gaba da kirkire-kirkire ganin yadda kasar ke da mutane masu fikira da tarin ilimin kimiyya da fasaha
- A wannan bangaren, Najeriya ta samu karuwa yayin da kamfanin Innoson suka fara kera keke napep na farko a Najeriya
- Jama'a da dama sun yi martani da ganin wannan kira ta gida, inda da dama suka tofa albarkacin bakinsu
Jihar Anambra - Kamfanin kera motoci A Najeriya, Innoson Vehicles Manufacturing (IVM) ya fitar da sabbin nau'ikan babura masu kafa uku ga kasuwannin Najeriya.
Baburan masu kujeru 5 masu suna IVM wanda aka fi sani da ‘Keke Napep’ sun shiga jerin kere-keren kamfanin, wadanda suka hada da Connect, Caris, G20 Smart, Ikenga, G40 da G80.
Hotunan baburan masu uku da aka kera a jihar Anambra sun yadu a shafin Facebook, inda jaridar Punch ta yada wasu hotunan kuma a shafin Twitter.
Kalli hotunan:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Martanin 'yan Najeriya
Legit.ng Hausa ta tattaro wasu daga cikin maganganun da 'yan Najeriya ke yi bayan ganin hotunan wannan sabon kira na keke napep.
Ga kadan daga ciki:
@MDOFFUTMX:
"Idan har gwamnati za ta iya zama kashin bayan wannan kamfani kamar yadda suka yi wa dangote, za su zama abin rubutawa gida."
@JamiuAlapo:
"Wannan 'Keke Napep' da kuka danganta da masana'antar ta Innoson, wani samfuri ne na Bajaj Auto Ltd da 'yan uwanta. Siffa, zane, zubi, launi, tsarin roba, tsarin kujeru, fitilu, da dai sauransu duk kwafin Bajaj ne. Don haka, Innoson kawai dai ya sarkafa sassan ne."
@AkinmadeOluseyi:
"Wannan zai iya zama mai ma'ana ne kawai idan alamar farashinsa zai iya zama kasa da na kasashen waje saboda babu kudin shigo da kaya."
@umar_sirnoosiee:
"Hakan zai kawo musu kudi fiye da motocin da suke kerawa wadanda ’yan Najeriya ba sa SAYA!!!"
@Tolbat3:
"Kyakkyawan cigaba. Mu kwace ayyukan yi daga kasar Sin, mu baiwa matasanmu."
Saboda tsabar gudu, Direban tirela ya kashe yara biyu a gaban shagon mahaifiyarsu
A wani labarin, Direban Tirela, Moshood Gbadamosi, ya hallaka yara biyu, Olamide Opeyemi da Damilola Opeyemi a garin Ilisan-Remo dake jihar Ogun ranar Juma'ar da ta gabata.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa wannan mumunan hadari ya auku ne gaban shagon mahaifiyarsu.
Wata makwabciya, Olayinka Oremuyiwa, ta bayyanawa manema labarai cewa yara hudu Direban ya buge yayinda suke tsaye bakin titi. Tace an garzaya da su asibitin koyarwan jami'ar Babcock kafin suka mutu.
Asali: Legit.ng