Gwamna Matawalle ya naɗa Sabbin Sarakuna da zasu maye gurbin waɗan da ya tsige

Gwamna Matawalle ya naɗa Sabbin Sarakuna da zasu maye gurbin waɗan da ya tsige

  • Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya naɗa sabbin sarakuna uku biyo bayan tsige wasu da zargin taimaka wa yan bindiga
  • Gwamnatin Zamfara ta gurafanar Sarakunan da ta tsige bisa zargin suna da alaƙa da ayyukan ta'addancin yan bindiga
  • Sarakunan da abun ya shafa sun haɗa da na Masarautar Zurmi da kuma takwaransa na masarautar Dansadau

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Zamfara - Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, ya naɗa sabbin sarakuna uku waɗan da zasu maye gurbin tsoffin da aka tsige da zargin hannu a ayyukan yan bindiga.

Jaridar Punch ta rahoto cewa Sarkin Zurmi, Abubakar Atiku, da takwarsa na masarautar Ɗansadau, Hussaini Umar, gwamna ya tsige su bisa zargin alaƙa da 'yan bindiga.

Gwamna Bello Matawalle.
Gwamna Matawalle ya naɗa Sabbin Sarakuna da zasu maye gurbin waɗan da ya tsige Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Sabbin sarakunan da gwamnatin ta naɗa sune, Alhaji Muhammed Suleiman Bello na masarautar Zurmi, Aliyu Garba Mafara, a masarautar Birnin Yandoto, da kuma Mohammed Aliyu na masarautar Bazai.

Kara karanta wannan

Titin Abuja-Kaduna: El-Rufa'i ya bada shawarar tayar da wasu garuruwa uku dake kan hanyar

A wata sanarwa da Sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Kabiru Balarabe, ya fitar, ya ce: "Naɗin sabbin sarakunan guda uku zai fara aiki ne nan take."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamnati ta gurfanar da Sarakunan da take zargi

Sarakuna biyu na Masarautun Dansadau da Zurmi, da aka kama kuma suke tsare a gidan gwamnati da ke Gusau, babban birnin Zamfara tsawon watanni, sun gurfana a gaban Kotu.

Gwamnatin jihar Zamfara karkashin gwamna Bello Matawalle ta gurfanar da sarakunan a gaban Kuliya bisa zargin hannu a ayyukan yan bindiga.

Sai dai rahotanni sun bayyana cewa yayin zaman Kotun an ba da belin Sarakunan kan wasu sharuddai.

A wani labarin kuma Tashin Hankali: An yi garkuwa da ɗalibai kwalejin horar da Malamai a jihar Kaduna

An yi garkuwa da ɗalibai hudu na kwalejin ili mi ta jihar Kaduna da ke Gidan Waya, ƙaramar hukumar Jema'a da yammacin Litinin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Zamfara ta kirkiro sabbin masarautu 2, jimillar masarautun jihar 19 a yanzu

A wata sanarwa da kungiyar ɗaliban Kaduna reshen makarantar ta fitar ta ce an sace daliban ne a Anguwar Mil ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262