Tashin Hankali: An yi garkuwa da ɗalibai kwalejin horar da Malamai a jihar Kaduna

Tashin Hankali: An yi garkuwa da ɗalibai kwalejin horar da Malamai a jihar Kaduna

  • An yi garkuwa da ɗalibai hudu na kwalejin ilimi ta jihar Kaduna da ke Gidan Waya, ƙaramar hukumar Jema'a da yammacin Litinin
  • A wata sanarwa da kungiyar ɗaliban Kaduna reshen makarantar ta fitar ta ce an sace daliban ne a Anguwar Mil ɗaya
  • Sanarwan ta bayyana cewa masu garkuwan sun nemi a tara musu kuɗaɗe masu ɗumbin yawa a matsayin kuɗin fansa kafin su sake su

Kaduna - Ɗaliban kwalejin ilimi ta jihar Kaduna (KSCOE) da ke gidan waya, ƙaramar hukumar Jema'a guda hudu sun shiga hannun masu garkuwa da mutane.

Daily Trust ta rahoto cewa an sace ɗaliban ne su hudu a Anguwar mil ɗaya da ke yankin Gidan Waya ranar Litinin da yamma.

Taswirar jihar Kaduna.
Tashin Hankali: An yi garkuwa da ɗalibai kwalejin horar da Malamai a jihar Kaduna Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A wata sanarwa da kakakin kungiyar ɗaliban jihar Kaduna (KADSSU) reshen KSCOE, Kwamaret Benjamin Fie, ya rattaba wa hannu, ya ce an sace ɗaliban ne da yammacin Litinin.

Kara karanta wannan

Bayan Kashe wacce ta zagi Annabi, Yan sanda sun gana da Malamai da masu ruwa da tsaki

Ya kara da cewa masu garkuwan da suka sace ɗaliban sun bukaci a ba su maƙudan kuɗaɗe a matsayin Fansa kafin su sake su.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce:

"Cikin ɓacin rai da takaici ƙungiyar ɗaliban jihar Kaduna reshen kwalejin ilimi na sanar wa sauran ɗalibai da al'umma baki ɗaya cewa an yi garkuwa da ɗalibai hudu."

A cewar kakakin ɗaliban kwalejin, waɗan da lamarin garkuwan ya rutsa da su sun haɗa da, Racheal Edwin, Esther Ishaya, Promise Tanimu, da kuma Beauty Luka.

Masu garkuwa sun nemi kuɗin fansa

Mai magana da yawun ɗaliban kwalejin ya ce:

"Masu garkuwan na bukatar makudan kudi a matsayin fansa kafin su sake su. Muna amfani da wannan damar wajen kira ga ɗalibia da sauran al'umma su taimaka da addu'a."

A wani labarin kuma Kashe Deborah a Sokoto: Yan sanda sun gana da Malaman Musulunci da masu ruwa da tsaki

Kara karanta wannan

Jerin yan takarar shugaban ƙasa a APC da suka sayi Fom N100m kuma suka gaza maida wa

Hukumar yan sanda reshen jihar Zamfara ta gana da Malaman addini da masu faɗa aji biyo bayan kashe ɗalibar da ta zagi Annabi SAW a Sokoto.

Kwamishinan yan sandan Zamfara, Ayubah Elkanah, ya yi kira ga mutane su giji ɗaukar doka a hannun su, su kai korafi ga hukumomin tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel