Dokar zabe: Kotun koli ta sa ranar da za a saurari karar Shugaban kasa da 'Yan Majalisa

Dokar zabe: Kotun koli ta sa ranar da za a saurari karar Shugaban kasa da 'Yan Majalisa

  • A makon gobe babban kotun koli a Najeriya za ta zauna domin sauraron shari’a a kan dokar zabe
  • Shugaban kasa da AGF sun kalubalanci sashe na 84 na sabuwar dokar zabe ta 2022 a gaban kotu
  • Ministan shari’a ya na so a yanke hukunci ne a kan sahihancin sashen dokar da ake ta rikici a kai

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Babban kotun Najeriya ya tsaida Alhamis, 26 ga watan Mayu 2022, a matsayin ranar da za a saurari kara a game da dokar zabe na shekarar 2022.

Tribune ta ce a mako mai zuwa kotun koli za ta zauna a kan wannan kara da Ministan shari’a, Abubakar Malami ya kawo, yana kalubalantar majalisa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da babban lauyan gwamnati, Abubakar Malami SAN, su na da ja a game da sashe na 84(12) na dokar zabe na Najeriya.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Ministar kudi ta dakatar da Akanta-Janar na tarayya don bincike kan badakalar naira biliyan 80

Kotun koli ta hada da Kwamishinan shari’an jihar Ribas da shugaban majalisar dokokin jihar bayan lauyoyi sun ce hukuncin da za a zartar zai shafe su.

Jihar Ribas ta shiga shari'ar

Mai shari’a Mohammed Musa Datijjo ya daga karar ne zuwa makon gobe bayan lauyan shugaban kasa, Prince Lateef Fagbemi (SAN) ya kawo bukatarsa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Prince Lateef Fagbemi (SAN) ya roki Alkalin kotun koli ya hada da gwamnatin jihar Ribas a shari’ar.

Abubakar Malami
AGF Abubakar Malami Hoto: @MalamiSAN
Asali: Twitter

Kayode Ajulo shi ne lauyan da yake kare majalisar tarayya. Shi kuma Emmanuel Ukala SAN shi ne wanda aka kawo domin ya tsayawa gwamnatin Ribas.

Sashe na 84 (12) ya ci karo da doka

Lauyoyin gwamnati da na ‘yan majalisa su na gardama ne kan sahihanci sashe na 84 (12) na dokar. AGF ya ce wannan sashe ya ci karo da tsarin mulki.

Kara karanta wannan

Jonathan ya amsa kiran masoyansa, yau za a gabatar da fam din shiga takararsa a APC

A dalilin haka babban lauyan na gwamnatin tarayya ya roki kotun koli ta goge bangaren dokar.

Premium Times ta ce Musa Dattijo-Mohammed da wasu Alkalai bakwai ne za su saurari wanan shari’a da zai yi tasiri a zabe mai zuwa da za a shirya a 2023.

A shari’ar mai lamba ta SC/CV/504/2022 da aka shigar a ranar 29 ga watan Afrilu, lauyan gwamnatin tarayya ya roki kotu ta shafe sashen dokar zaben

Aminin Buhari zai nemi Gwamna

A makon nan aka ji labari Hon. Farouk Adamu Aliyu ya fito neman takarar gwamna a jihar Jigawa a karkashin jam’iyyar APC domin ya gaji Badaru Abubakar.

Tsohon ‘dan majalisar ya yi kira ga Gwamnan na Jigawa ya bari ayi adalci wajen fito da ‘dan takara. Aliyu ya taba rike shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel