Ke duniya: 'Yan sanda sun damke magidanci da ya tura matarsa karuwanci, ya siyar da 'dan shi

Ke duniya: 'Yan sanda sun damke magidanci da ya tura matarsa karuwanci, ya siyar da 'dan shi

  • 'Yan sanda sun yi ram da wani mutumi mai shekaru 36, Kingsley Essien bisa zarginsa da safarar matarsa zuwa Mali da kuma sai da 'dansa mai shekaru biyu a kan N600,000
  • Matar ta bayyana yadda ya ma ta karya da cewa ya samar ma ta aiki a Bamako, Mali sannan zai taimake ta wajen kai ta kasar don neman abun rayuwa
  • Sai dai, da isarta ta fahimci yadda ya siyar da ita ga wani masana'antar safarar mutane a kan N1.4m inda aka tilasta ma ta karuwanci daga bisani ta samu damar tserowa zuwa Najeriya

Ogun - Rundunar 'yan jihar Ogun a ranar Alhamis sun tabbatar da kama wani mutum mai shekaru 36, Kingsley Essien, bisa zarginsa da safarar matarsa zuwa Mali, gami da siyar da 'dansa mai shekaru biyu akan N600,000.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Ministar kudi ta dakatar da Akanta-Janar na tarayya don bincike kan badakalar naira biliyan 80

The Nation ta ruwaito cewa, kakakin 'yan sanda jihar, DSP Abimbola Oyeyemi, ya sanar da hakan a wata takarda da ya bayyanawa manema labarai a Ota dake Ogun.

Ke duniya: 'Yan sanda sun damke magidanci da ya tura matarsa karuwanci, ya siyar da 'dan shi
Ke duniya: 'Yan sanda sun damke magidanci da ya tura matarsa karuwanci, ya siyar da 'dan shi. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Oyeyemi ya bayyana yadda aka yi ram da wanda ake zargin bayan wani rahoto da matar wanda ake zargin, Bright Essien ta shigar ga hedkwatar 'yan sanda ta marabar Agbara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Matar ta ruwaito yadda a wani lokaci a watan Oktoba 2021, mijinta Kingsley Essien, ya sanar ma ta da cewa ya samar ma ta aiki a Bamako, Mali, sannan ya taimaka wa mutane da dama a baya wajen tafiya kasar don neman abun rayuwa.

Ta kara da cewa, kasancewarsa mijinta, ba ta yi zargin wani abu mara kyau ba, har sai da ta isa Mali inda ta fahimci cewa mijin nata ya siyar da ita a kan N1.4 miliyan ga wata masana'antar safarar mutane, wanda wata mata ke jagoranta.

Kara karanta wannan

Yada barna: Gwamnatin Buhari ta gana da Facebook, ta nemi kassara lagon IPOB a kafar

"Yayin da take kasar Mali, an tilasta ma ta karuwanci, daga bisani ta nemi ofishin jakadancin Najeriya a Bamako inda aka taimaka ma ta wajen maido ta Najeriya.
"Bayan dawowar ta Najeriya, ta fahimci cewa 'danta mai shekaru biyu wanda ke karkashin kulawan mijinta, ya yi batan-dabo babu amo ba labarinsa," a cewarta.

Kakakin ya ce an shigar da rahoton ne ga DPO marabar Agbara, SP Abiodun Salau, wanda ya samar da jami'ansa inda suka bi bayan wanda ake zargin, daga bisani suka damko shi.

Ya kara da cewa yayin da aka kama shi, wanda ake zargin ya amsa laifinsa. Sannan ya kara da cewa ya siyar da 'dansu mai shekaru biyu ga wani a kan N600,000, jaridar Independent ta rahoto hakan.

Sai dai, kwamishinan 'yan sandan jihar, (CP) Mr Lanre Bankole, ya yi umarni da mika wanda ake zargin sashin yaki da safarar mutane na yankin binciken laifuka da sashin binciken sirri don cigaba da bincike.

Kara karanta wannan

Hanyar Abuja-Kaduna: A jiya Talata kadai, mutum 20 sun kone kurmus a hadarin mota, yan bindiga sun sace 30

Haka zalika, CP ya yi umarci 'yan sanda da zakulowa gami da damko wanda ake zargin ya siya yaron don gano inda yake.

Asali: Legit.ng

Online view pixel