Nasara: Sojoji sun kai farmaki maboyar ‘yan IPOB, sun kwato makamai da tarin alburusai

Nasara: Sojoji sun kai farmaki maboyar ‘yan IPOB, sun kwato makamai da tarin alburusai

  • Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar gano wata mafakar 'yan ta'addan IPOB a yankin Kudu maso Gabas
  • Jami'an sun kwato makamai da wasu kayayyakin aikata laifi daga hannun tsagerun da ake zargin 'yan ESN da IPOB ne
  • Jami'an tsaro sun bayyana cewa, suna ci gaba da samun hadin kai daga mazauna yankin wajen samun bayanan 'yan ta'adda

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Imo - Wani rahoton Vanguard ya ce, rundunar sojin Najeriya ta ce ta samu nasarar kwato tarin makamai da harsasai na wasu da ake zargin 'yan kungiyar IPOB ne da kuma ESN a yankin Kudu.

Kakakin rundunar, Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, Premium Times ta ruwaito.

Sojin Najeriya sun farmaki IPOB
Nasara: Sojoji sun kai farmaki maboyar ‘yan IPOB, sun kwato makamai da tarin alburusai | Hoto: thecable.ng
Asali: Facebook

Ya ce an kwato makaman da alburusai ne a wani samame da jami'ai suka kai maboyar kungiyar a hanyar Amaifeke zuwa Akkatta a karamar hukumar Orlu a jihar Imo, a Kudu maso Gabashin Najeriya.

Kara karanta wannan

Adamawa: 'Yan sanda sun budewa masu garkuwa da mutane wuta, sun halaka 3

Ya bayyana cewa, rundunar sojin ta tsallake kwanton baunan 'yan ta'addan kafin daga bisani ta kwato mota dauke da makamai da tsagerun suka tsallake suka gudu. Kana an kwato buhun bama-bamai da wata mota kirar Toyota Camry makare da kayayyakin laifi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nwachukwu ya ce dakarun birgediya ta 34 na rundunar sojojin Najeriya ne suka kai farmakin.

Sai dai bai bayyana lokacin da aka gudanar da aikin ba.

Rundunar ta yabawa jama’a kan yadda suke ci gaba da baiwa sojoji da sauran jami’an tsaro goyon baya da hadin kai a yakin da suke yi da aikata laifuka a kasar.

Rundunar ta ce kungiyar IPOB ta “gallazawa ‘yan kabilar Igbo da sauran ‘yan Najeriya da ba su ji ba ba su gani ba,” a kokarinsu na kakaba dokar zaman gida ga al’ummar Kudu maso Gabas.

Ya bukaci mazauna yankin da su ci gaba da bayar da “sahihan bayanai masu inganci” don tallafawa ayyukan da ake yi na maido da zaman lafiya da tsaro a yankin, da kuma sauran sassan kasar da ke fama da rikici da tashin-tashina.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Sojoji sun kashe wani kasurgumin kwamandan Boko Haram

Nasara daga Allah: Sojoji sun kashe wani kasurgumin kwamandan Boko Haram

A wani labarin, dakarun sojin Najeriya da ke aiki da Operation Hadin Kai, sun kashe wani kasurgumin kwamandan Boko Haram Abubakar Sarki a dajin Sambisa, da ke Yuwe a karamar hukumar Konduga a jihar Borno, Daily Trust ta ruwaito.

Jami’an rundunar a wani samame na hadin gwiwa da suka kai a lokacin da suke gudanar da aikin share fage, sun kuma kashe Amir kuma shugaban yankin Gaita na 'yan ta'addan, Malam Shehu da wasu dakarunsa.

Kakakin rundunar soji, Maj.-Gen. Benard Onyeuko ne ya bayyana hakan ga manema labarai a hedikwatar tsaro da ke Abuja yayin da yake bayar da bayanai kan nasarorin da sojojin suka samu a fadin kasar tsakanin 28 ga Afrilu zuwa 19 ga Mayu 2022.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.