Tashin hankali: An kaure da rikici tsakanin 'yan acaba da 'yan sanda a jihar Legas
- Rikici ya barke a jihar Legas yayin da 'yan sanda ke kokarin tilastawa 'yan acaba bin dokar hana zirga-zirga
- Hanin na zuwa ne bayan da wasu 'yan acaba suka lakadawa wani mawaki duka har ya mutu a wani yankin jihar
- Majiyoyi sun bayyana cewa, rikicin ya kai ga toshe hanya da kuma tara cunkoson ababen hawa a wani titi
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jihar Legas - An shiga tashin hankali a karamar hukumar Ojo da ke jihar Legas kan yunkurin da ‘yan sanda ke yi na tilasta dokar gwamnatin jihar ta hana acaba a wasu yankunan jihar.
A ranar Larabar da ta gabata ne gwamnatin jihar ta fitar da dokar hana zirga-zirgar 'yan acaba a kananan hukumomi shida na jihar sakamakon kisan wani mawaki mai suna David Imoh a Lekki, kamar yadda jaridar Guardian ta ruwaito.
An samu labarin cewa ‘yan sanda daga ofishin ‘yan sanda na Onireke, Ojo, sun damke wasu baburan acaba da ke aiki a kan hanyar Mile 2 zuwa Badagry, matakin da 'yan acaban suka bijirewa.
'Yan acaban sun yi yunkurin mamaye tashar tare kokarin kubutar da wasu daga cikin mambobinsu da ‘yan sandan suka kama.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun banka wuta a tsakiyar titi, yayin da wasu masu ababan hawa suka bar ababen hawansu a gefen titi sakamakon rikicin.
Rikicin ya haifar da turmutsitsi yayin da masu tafiya a kafa suka gudu saboda fargabar tashin-tashina
Hakazalika, lamarin ya haifar da dagulewar zirga-zirgar ababen hawa a bangarorin biyu na hanyar, rahoton Daily Trust.
Yayin da ’yan sandan suka yi harbin iska don tarwatsa 'yan acaban, sun yi wa jami’an ruwan duwatsu, inda 'yan sanda suka fara bin su a guje.
Ya zuwa yanzu dai adadin mutanen da dama sun samu raunuka daban-daban a yayin da suke kokarin tserewa daga yankin da rikicin ya barke.
Yanzu haka an tura tawagar jami’an ‘yan sandan kwantar da tarzoma tare da wasu sojoji domin dawo da zaman lafiya a yankin.
Gwamnati Ta Haramta Yin Acaba a Ƙananan Hukumomi 6 a Legas
A wani labarin, gwamnatin Jihar Legas ta haramta yin haya da babur wato acaba a kananan hukumomi shida na jihar, rahoton Channels Television.
Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Legas ne ya sanar da hakan yayin da ya ke yi wa hukumomin tsaro a jihar jawabi a ranar Laraba, rahoton The Cable.
Kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Ikeja, Surulere, Eti Osa, Lagos Mainland, Lagos Island da Apapa.
Asali: Legit.ng