Yanzu: Gwamnati Ta Haramta Yin Acaba a Ƙananan Hukumomi 6 a Legas

Yanzu: Gwamnati Ta Haramta Yin Acaba a Ƙananan Hukumomi 6 a Legas

  • Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo Olu ya sanar da dokar haramta acaba a wasu kananan hukumomi shida a jiharsa
  • Kananan hukumomin sun kunshi Ikeja, Surulere, Eti Osa, Lagos Mainland, Lagos Island da Apapa
  • Sanwo Olu ya ce dokar za ta fara aiki ne a ranar 1 ga watan Yunin shekarar 2022, yana mai gargadin masu acabar su sauya sana'a ko su bar jihar

Jihar Legas - Gwamnatin Jihar Legas ta haramta yin haya da babur wato acaba a kananan hukumomi shida na jihar, rahoton Channels Television.

Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Legas ne ya sanar da hakan yayin da ya ke yi wa hukumomin tsaro a jihar jawabi a ranar Laraba, rahoton The Cable.

Yanzu: Gwamnati Ta Haramta Yin Acaba a Kananan Hukumomi 6 a Legas
Gwamnati Ta Hana Yin Acaba a Kananan Hukumomi 6 a Legas. Hoto: The Cable.
Asali: Twitter

Kananan hukumomin da dokar ta shafa

Kara karanta wannan

Hanyar Abuja-Kaduna: A jiya Talata kadai, mutum 20 sun kone kurmus a hadarin mota, yan bindiga sun sace 30

Kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Ikeja, Surulere, Eti Osa, Lagos Mainland, Lagos Island da Apapa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamnan ya ce dokar za ta fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Yuni, ya kara da cewa ba mu son ganin dukkan baburan haya a manyan tituna.

"Dokar hana acaba a manyan tituna a wadannan kananan hukumomin za ta fara aiki a ranar 1 ga watan Yuni. Wannan shine mataki na farko na haramta babura za muka fara domin wasu su sani, cikin kankanin lokaci, su fita ko su nemi wata sana'ar," in ji gwamnan.
"Daga ranar 1 ga watan Yuni, za mu lissafa dukkan unguwannin da abin zai shafa a kananan hukumomin. Yanzu muna sanarwa. Don haka kowa na iya bullowa da tsarin cimma hakan. Daga ranar 1 ga watan Yuni, ba mu son ganin yan acaba a dukkan manyan tituna."

Kara karanta wannan

Batanci: Ku girmama addinin mutane da abinda suka yi imani da shi sai a zauna lafiya, El-Rufa'i

An saka dokar ne kwanaki kadan bayan yan acaba sun halaka wani injiniya kan N100

Wannan dokar haramta acabar na zuwa ne kwanaki kadan bayan wasu yan acaba sun hallaka wani injiniyan sauti mai suna David Imoh a unguwar Lekki ta Jihar Legas.

Rashin jituwa kan canjin N100 na ya shiga tsakaninsu, hakan yasa wasu yan acaba da ke wurin suka taru suka yi wa David da wasu abokansa duka.

Yan acaban sun cinna wa David wuta bayan sun masa duka ya suma.

Benjamin Hundeyin, kakkakin yan sandan Jihar Legas, ya ce an kama mutum hudu kan zargi da hannu wurin kashe injiniyan.

Ƙungiyar CAN Za Ta Yi Gagarumin Zanga-Zanga Na Ƙasa Kan Kisar Deborah Samuel

A wani rahoton, kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, ta bukaci a yi zanga-zanga na kasa bisa kisar da aka yi wa Deborah Samuel, dalibar aji 2 na Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sokoto, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Gwamnatin Kano Ta Magantu Kan Fashewar Tulun Gas, Ta Ce Ba a Makaranta Abin Ya Faru Ba

Shugaban CAN, Rabaran Olasupo Ayokunle, cikin wasikar da ya aike wa dukkan shugabannin kungiyar, ya bukaci kiristoci su yi zanga-zangar lumana a harabar cocinsu a ranar Lahadi 22 ga watan Mayun 2022.

Ya yi kirar ne bayan kisa da kona wata daliba da fusatattun matasa suka yi bayan zarginta da furta kalaman batanci ga Annabi Muhammadu (SAW).

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel