Atiku: Da Zarar Na Zama Shugaban Ƙasa Ƴan Bindiga Za Su 'Shiga Uku'

Atiku: Da Zarar Na Zama Shugaban Ƙasa Ƴan Bindiga Za Su 'Shiga Uku'

  • Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa, ya ce idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa sai ya tabbatar ‘yan ta’adda sun rasa wurin buya
  • A ranar Laraba ya bayyana wa wakilan jam’iyyar PDP a Katsina cewa rashin jajircewar shugabanni ne ya bai wa ‘yan ta’adda damar numfasawa
  • Ya yi alkawarin cewa in har aka mara masa baya har ya dare kujerar shugaban kasa a 2023, sai ya fi mayar da hankali bangaren rashin tsaro yadda zaman lafiya zai dawo ko ina

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Katsina - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce in har aka zabe shi a matsayin shugaban kasar Najeriya, zai tabbatar ‘yan bindiga sun rasa maboya, Daily Trust ta ruwaito.

Atiku ya yi wannan bayanin ne a ranar Laraba yayin yin jawabi ga wakilan jam’iyyar PDP a Katsina inda ya ce laifin shugabanni ne har ta kai ga ‘yan ta’adda su na walwala.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Ni nafi cancanta na gaji Buhari, in ji Saraki

Atiku: Da Zarar Na Zama Shugaban Ƙasa 'Yan Bindiga Za Su 'Shiga Uku'
Atiku: Da Zarar Na Zama Shugaban Ƙasa 'Yan Bindiga Za Su Rasa Wurin Boyewa. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a 2023, zai tabbatar ya kawo karshen duk wani ta’addanci yayin da duk mutanen kirki za su koma cikin zaman lafiya da walwala.

Kamar yadda Premium Times ta nuna, ya shaida cewa:

“Muna hanyarmu ta zuwa Katsina tare da tsohon gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Shema a jirgina, babu inda ba ma gani a kasa. Ina dajikan da ake cewa ‘yan ta’adda sun boye an kasa gano inda su ke?.
“Ina mai tabbatar muku da cewa in har ku ka ba mu goyon bayan na zama shugaban kasa, na yi alkawarin cewa rashin tsaro zai zama tarihi.”

Ya bayyana muhimman bangarorin da zai fi mayar da hankali

Atiku ya haska bangarorin da zai mayar da hankali akai inda ya ce zai tabbatar da an samar da hadin kai, tattalin arziki, ilimi da sauransu.

Kara karanta wannan

2023: Saura kwana 10 zabe, an shiga yamutsi a PDP game da wanda za a tsaida takara

Ya yi godiya ga wakilan jam’iyyar akan hadin kan da su ka ba su a 2019 a Port Harcourt, babban birnin Jihar Ribas akan cewa sun taimaka masa wurin haskawa a cikin sauran ‘yan takara wurin daga martabar jam’iyyar.

A wadanda su ka raka shi akwai Chief Raymond Dokpesi, Sanata Baraka Sani, Sanata Abdul Ningi, Alhaji Adamu Maina Waziri da tsohon sakataren jam’iyyar PDP, Umar Tsauni.

'Batanci: Atiku Ya Ce Ba Shine Ya Wallafa Rubutun Sukar Kashe Ɗalibar Sokoto a Shafinsa Ba

A wani rahoton, Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP ya nisanta kansa daga yin ala-wadai akan kisan Deborah Samuel.

Deborah dalibar aji biyu ce a kwalejin ilimi ta Shehu Shagari da ke Jihar Sokoto, kuma kirista ce, an halaka ta ne bisa zarginta da yin batanci ga Annabi Muhammad SAW.

Sai dai Atiku ya yi wata wallafa a Twitter inda ya ce:

Kara karanta wannan

Matashi ‘Dan shekara 38 ya fito zai jarraba sa'a a takarar Shugaban kasa a zaben 2023

“Babu adalci dangane da kisan muguntar da aka yi mata. An halaka Deborah Yakubu kuma wajibi ne a kwatar mata hakkinta akan wadanda su ka halaka ta. Ina mai yi wa ‘yan uwanta da kawayenta ta’aziyya.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel