A ‘yan watanni, simintin Dangote ya saida kayan N413bn, ya tashi da ribar Biliyoyin kudi

A ‘yan watanni, simintin Dangote ya saida kayan N413bn, ya tashi da ribar Biliyoyin kudi

  • Ana tunanin kamfanin Dangote Cement PLC ya yi cinikin da ya kusa kai na rabin Tiriliyan a bana
  • Dangote Cement sun samu N410bn daga farkon shekarar 2022 zuwa karshen watan Maris dinnan
  • Idan aka cire harajin da aka biya gwamnatin Najeriya, tsantsar ribar da aka samu ta zarce N100bn

Lagos - Daily Nigerian ta ce cinikin kamfanin Dangote Cement ya karu da kashi 24.2% a cikin watannin farkon wannan shekarar ta 2022 da ake ciki.

Ribar da kamfanin ya samu a shekarar nan ya karu da 18%, idan aka cire harajin da aka biya.

Bayanai sun fara nuna cewa daga farkon Junairun nan zuwa ranar 31 ga watan Maris 2022, kudin da ya shiga asusun kamfanin ya kai Naira biliyan 413.

Haka zalika Dangote Cement ya samu ribar Naira biliyan 105.9 idan aka cire abin da aka biya na haraji. Ba a kammala lissafin wadannan kudi ba tukun.

Kara karanta wannan

Sokoto: An ayyana neman wadanda aka gani a bidiyon kone dalibar da ta zagi Annabi

Daga Junairu zuwa watan Maris, kamfanin ya saida metric ton 7.2 na siminti a fadin Afrika. A Najeriya kadai abin da aka saida ya doshi metric ton 4.8.

Mun ci riba duk da matsaloli - CEO

Shugaban kamfanin, Michel Puchercos ya bayyana cewa sun shiga wannan shekarar da kafar dama, su na samun riba duk da kalubalen da ake samu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Simintin Dangote
Buhunan simintin Dangote Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Michel Puchercos ya shaida cewa ribar da aka samu ta sa kamfanin ya samu kudi a kasar nan.

A cewar jami’in kamfanin, ribar da aka samu bayan cire abin da aka biya na haraji ya karu da 18.6%. Hakan na nufin a watanni uku, an ci ribar N105.9bn.

Puchercos ya tabbatar da cewa ana kokarin fara aiki a kamfanin Okpella, sannan an yi nisa wajen zuba na’urorin kawo siminti a kasar Ghana da Cote d’Ivoire.

Kara karanta wannan

Rundunar Sojin Saman Najeriya, NAF, Ta Ɗage Bikinta Saboda Fashewar 'Tulun Gas' a Kano

Ana rububin siminti - Michel Puchercos

Ana samun miliyoyin mutane da ke neman siminti, kamfanin ya na ganin zai iya sharewa mutane hawaye duk da kalubalen da kasuwa ta ke fuskanta.

Rahoton PM News ya ce a Afrika babu kamfanin simintin da ya fi na Dangote da ke Obajana, jihar Kogi. Kamfanin zai iya samar da metric ton 51 duk shekara.

Bayan nan akwai wasu kamfanonin a garuruwan Ibese a Ogun, Gboko a Benwai da na Okpella. Wannan ya sa ake iya fita da siminti zuwa kasashen waje.

Manufar Tein TS Jack-Rich

Ku na da labari cewa Tein TS Jack-Rich wanda yake neman zama shugaban kasa a karkashin APC, ya sake jaddada cewa zai bunkasa tattalin arzikin kasa.

TS Jack-Rich ya ce muddin ya zama shugaban Najeriya, gwamnatinsa ba za ta ci bashin ko sisi ba, sannan zai nemawa matasan kasar nan hanyar cin abinci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng