Rundunar Sojin Saman Najeriya, NAF, Ta Ɗage Bikinta Saboda Fashewar 'Tulun Gas' a Kano
- Rundunar Sojin Saman Najeriya, NAF, ta dage bikinta da aka shirya yi a ranar Alhamis zuwa Asabar a Kano.
- Mai magana da yawun NAF, Edward Gabkwet, ya ce an dage bikin ne saboda afkuwar wasu abubuwa da ba a yi tsammani ba
- Amma, wani babban jami'i na NAF, ya bayyana cewa fashewar 'tulun gas' din a Kano ne ya sa aka dage taron don kara inganta tsaro
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Mahukunta na Rundunar Sojojin Saman Najeriya, NAF, sun dage bikin da aka shirya yi a Kano na shekarar 2022.
Daily Trust ta rahoto cewa da farko an shirya yin bikin ne a ranar Alhamis amma an matsar da shi zuwa ranar Asabar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Duk da cewa kakakin NAF, Edward Gabkwet, wanda ya fitar da sanarwar a Abuja bai bayyana dalilin dage bikin ba, wani babban jami'i na rundunar ya ce fashewar abu a Kano ne dalilin.
Jami'in ya ce:
"Bayan fashewar abu a Sabon Garin Kano a yanzu, unguwar da za a yi bikin mu na 2022, akwai bukatar mu sake karfafa tsaro a yankin kafin fara bikin don gudun abin da ka iya faruwa."
Daily Trust ta rahoto cewa a kalla mutane uku ne suka mutu sakamakon fashewar abin kuma a yanzu wasu gini ya danne su.
Amma, yayin fitar da sanarwar, Gabkwet, mai mukamin Air Commodore, ya ce an dage bikin ne 'saboda wasu abubuwa da ba a yi tsammanin faruwarsu ba."
Ya ce:
"Bikin Ranar Rundunar Sojin Saman Najeriya, NAF, na 2022 da aka shirya yi daga ranar 19 - 21 ga watan Mayu a NAF Base, Kano yanzu an dage shi zuwa ranar 21 - 23 na Mayun 2022 a wurin da aka shirya yi tunda farko.
"An yi canjin ne saboda faruwar wasu abubuwa da ba a yi tsammani ba. NAF tana bawa dukkan bakin da aka gayyata hakuri don abin da canjin zai haifar musu."
Saurari karin bayani ...
Asali: Legit.ng