Gbemisola Saraki ta maye gurbin Amaechi a matsayin ministan sufuri
- A ranar Litinin, 16 ga watan Mayu ne Rotimi Amaechi ya sauka daga mukaminsa na ministan sufuri
- An tattaro cewa a yanzu karamar ministar sufuri Gbemisola Saraki ce ta maye gurbinsa wajen tafiyar da harkokin ma'aikatar
- Amaechi dai yana neman takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa karkashin inuwar jam'iyyar APC mai muki
Rahoton Business Day ya kawo cewa karamar ministar sufuri, Gbemisola Saraki, ta karbi ragamar aiki daga hannun Rotimi Amaechi a matsayin ministar sufuri bayan ya yi murabus a hukumance a ranar Litinin, 16 ga watan Mayu.
Gbemisola ta kasance kanwa ga babban dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party mai adawa a kasar.
Amaechi ya yi murabus daga mukaminsa na ministan sufuri domin ya mayar da hankali ga kudirinsa na takarar shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A takardar ajiye aikinsa mai kwanan wata 16 ga watan Mayu 2022, zuwa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, Amaechi ya ce ya yi murabus ne domin yin takara a zabe mai zuwa.
A wasikar ajiye aiki da ya mika, Vanguard ta nakalto Amaechi yana cewa:
“Cike da nauyin zuciya ne nake mika takardar ajiye aikina a matsayin ministan sufuri na tarayyar Najeriya don yin takarar tikitin shugaban kasa na jam’iyyarmu All Progressives Congress mai albarka.
“Mai girma shugaban kasa, ya kasance babban abin alfahari da alfarma kasancewa mamba a majalisar ministocin ka bayan nasarar da ka samu a zaben 2015 mai cike da tarihi. A karkashin mulkinka, ma’aikatar sufuri ta samu gagaruman nasarori, ta hanyar goyon bayanka da jajircewa wajen tabbatar da ganin cewa mun sauke hakkinmu.
“Yayin da na shiga mataki na gaba na manufar mu na yin aiki don samar da ingantacciyar Najeriya ga daukacin ‘yan Najeriya, ina neman addu’o’i da albarkar mai girma shugaban kasa, sannan ina duba ga ci gaba da samun goyon bayanka.
"Ranka ya dade yayin da nake neman ka yi la’akari da bukatata don Allah ka yarda da tabbacin girmamawa na."
Shekarau Ya Fita Daga APC, Ya Koma NNPP Ya Haɗe Da Kwankwaso
A wani labarin, Sanata Ibrahim Shekarau, mai wakiltar Kano ta Tsakiya ya fita daga jam'iyyar APC mai mulki a kasa ya koma NNPP mai kayan marmari, rahoton aminiyya.
Tsohon gwamnan na Kano ya fice ne karkashin jagorancin tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso, jigo na kasa a jam'iyyar ta NNPP.
Yakubu Yareema, wani na hannun daman Malam Shekarau ya sanar da hakan a yammacin ranar Talata kamar yadda Freedom Radio ta rahoto.
Asali: Legit.ng