Yanzu-Yanzu: Daya daga manyan hadiman Buhari ya yi murabus, zai yi takarar gwamna
Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin Neja Delta, Sanata Ita Enang, ya yi murabus daga mukaminsa domin ci gaba da neman kujerar gwamna a jihar Akwa Ibom.
Enang ya yi aiki a matsayin mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan majalisar dattijai tsakanin 2015 zuwa 2019.
Daga nan ne shugaba Buhari ya nada shi a matsayin mai taimaka masa kan harkokin Neja Delta a 2019.
A cikin wata sanarwa a ranar Litinin, wadda Leadership ta ce ta samu, mai taimaka wa Enang kan harkokin yada labarai, Edet Ekpenyong, ya ce tsohon dan majalisar ya gode wa shugaba Buhari da ya ba shi damar yin aiki a karkashinsa.
A cewar Enang:
“Lokaci ya yi. Na yi niyyar tsayawa takarar gwamnan jihar Akwa Ibom a karkashin jam’iyyarmu ta APC, wadda a yanzu nake neman tsayawa takara, bayan da na saya na mika fom din tsayawa takara da nuna sha’awa.
"A kan haka na mika takardar murabus dina daga ofis, domin ci gaba da gudanar da takarar gwamna."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ku dakaci karin bayani...
Asali: Legit.ng