Daga karshe: Duk da kama Magu da aikata rashawa, gwamnati ta kara masa matsayi

Daga karshe: Duk da kama Magu da aikata rashawa, gwamnati ta kara masa matsayi

  • Hukumar aikin 'yan sanda ta kara wa wasu manyan jami'anta girma zuwa manyan mukamai a rundunar 'yan sanda
  • Daga cikinsu, akwai Mustafa Ibrahim Magu, wanda ya taba jagorantar hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC
  • Hakazalika, hukumar ta kuma karawa wasu jami'ai 23 girma,kamar yadda wata sanarwa da hukumar ta fitar ta bayyana

Abuja - Hukumar aikin ‘yan sanda ta tabbatar da karin girma ga tsohon shugaban riko na hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Mustafa Ibrahim Magu zuwa mataimakin sufeto janar na ‘yan sanda, tare da wasu mutane biyar.

AIG Magu Ibrahim wanda ke gargarar yin ritaya, shi ne wanda ya fi kowa girma a tsararrakinsa kuma ya kasa samun karin girma har sau biyu bayan da ya dawo hukumar ‘yan sanda daga EFCC, Channels Tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kisan Deborah: Kungiya ta nemi a kamo limamin BUK bisa zargin halasta jinin Bishop Kukah

Magu ya samu karin matsayi
Rudani: Duk da kama Magu da aikata rashawa, gwamnati ta kara masa matsayi | Hoto: dailytrust.com
Asali: Twitter

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar ta tabbatar da karin girma ga John Ogbonnaya Amadi a matsayin mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda, domin maye gurbin marigayi DIG Joseph Egbunike wanda ya wakilci Kudu Maso Gabas a tawagar ‘yan sanda.

Haka kuma an kara wa Zana Bala Senchi zuwa matsayin DIG, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sauran wadanda aka karawa girma zuwa AIG su ne CP Abraham Egong Ayim; Okunlola Kola Kamaldeen; Andrew Amieengheme; Akeera Mohammed Yous; Celestine Amechi Elumelu; Ngozi Vivian Onadeko da Danladi Bitrus Lalas (Airwing).

A wata sanarwa da Ikechukwu Ani, shugaban yada labarai da hulda da jama’a na hukumar ya fitar, ya ce an kara wa mataimakan kwamishinonin ‘yan sanda 23 girma zuwa kwamishinonin ‘yan sanda.

A karshe fadar Shugaban kasa ta magantu kan rade-radin yiwa Magu karin girma zuwa AIG

Kara karanta wannan

Deborah Samuel: Ƴan Najeriya Sun Yi Wa Ɗan Tsohon IGP Martani Kan Kalamansa Game Da Kisar Ɗalibar Sokoto Da Ta Zagi Annabi

A wani labarin, fadar shugaban kasa ta mayar da martani game da ikirarin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na shirin yiwa tsohon shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, karin girma zuwa mukamin AIG.

A cikin wata sanarwa da Garba Shehu, mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, ya fitar a ranar Alhamis, 8 ga watan Yuli, fadar shugaban kasar ta bayyana karara cewa alhakin yiwa jami’ai karin girma ya rataya ne kan Hukumar Kula da Ayyukan ’Yan Sanda, ba a kan Shugaba Buhari ba, Channels TV ta ruwaito.

Shehu ya ci gaba da cewa Buhari ba shi da hannu ko kadan a daga darajar jami'an 'yan sanda a kasar, Vanguard ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.