Da duminsa: A karshe fadar Shugaban kasa ta magantu kan rade-radin yiwa Magu karin girma zuwa AIG

Da duminsa: A karshe fadar Shugaban kasa ta magantu kan rade-radin yiwa Magu karin girma zuwa AIG

  • A cewar fadar shugaban kasa, ikirarin cewa Shugaba Buhari ya duba yiwuwar yiwa Ibrahim Magu karin girma karya ne
  • Fadar shugaban kasa ta bayyana hakan ne ga ‘yan Najeriya a cikin wata sanarwa da ta raba wa manema labarai a ranar Alhamis, 8 ga watan Yuli
  • Garba Shehu ya bayyana cewa shugaban kasar baya shiga kuma ba zai iya tsunduma baki cikin lamuran hukumar yan sanda ba

Fadar shugaban kasa ta mayar da martani game da ikirarin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na shirin yiwa tsohon shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, karin girma zuwa mukamin AIG.

A cikin wata sanarwa da Garba Shehu, mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, ya fitar a ranar Alhamis, 8 ga watan Yuli, fadar shugaban kasar ta bayyana karara cewa alhakin yiwa jami’ai karin girma ya rataya ne a kan Hukumar Kula da Ayyukan ’Yan Sanda, ba a kan Shugaba Buhari ba, Channels TV ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Fadar Shugaban kasa ta yi hasashen abunda zai faru da PDP a babban zaben 2023

Da duminsa: A karshe fadar Shugaban kasa ta magantu kan rade-radin yiwa Magu karin girma zuwa AIG
Garba Shehu ya ce PDP ta kirkiri karya don ta dace da burinta Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Shehu ya ci gaba da cewa Buhari ba shi da hannu ko kadan a daga darajar jami'an 'yan sanda a kasar, Vanguard ta ruwaito.

Wani bangare na jawabin na cewa:

“Kamar yadda kuke gani, Jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta tashi daga can, tana fitar da daya daga cikin irin wadannan sakwannin da aka watsa ba tare da tunani ba.
“Shugaba Buhari, ko kuma wani Shugaban Najeriya, ba shi da alhakin yin karin girma a rundunar ‘Yan Sanda. Wannan shine aikin hukumar yan sanda."

PSC ta hana Magu karin girma, ta bayyana umarnin wanda take jira

A baya Legit.ng ta kawo cewa, ukumar kula da lamurran 'yan sanda (PSC), a ranar Alhamis ta yi watsi da kudirin karin girma ga tsohon mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Ibrahim Magu.

KU KARANTA KUMA: Masu zanga-zangar ‘BuhariMustGo’ sun kai karar Ministan Buhari da Shugaban DSS a kotu

Hukumar ta ce tana jiran umarni daga ofishin antoni janar na tarayya da ministan shari'a tare da sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Daily Trust ta wallafa.

Wannan sanarwan na kunshe a wata takarda da aka baiwa manema labarai ta hannun kakakin hukumar, Ikechuckwu Ani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng