Yan bindiga sun sace Ɗan majalisar jiha a yankin mazaɓar Gwamnan Anambra

Yan bindiga sun sace Ɗan majalisar jiha a yankin mazaɓar Gwamnan Anambra

  • Wasu miyagun yan bindiga sun sace ɗan majalisar jiha mai wakiltar Aguata 1 a majalisar dokokin jihar Anambra, sun bar motarsa
  • Kakakin hukumar yan sanda na jihar, Mista Ikenga, ya tabbatar da lamarin, ya ce jami'an sun bazama neman kubutar da shi
  • Ya kuma musanta labarin da mutane ke yaɗawa cewa wani ɗan Bijilanti da aka gano gawarsa ɗan sanda ne

Anambra - Hukumar yan sanda ta jihar Anambra ta tabbatar da sace, Okechukwu Okoye, ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Aguata 1 a majalisar dokokin jihar Anambra.

Honorabul Okoye, wanda ɗan asalin garin Isoufia ne inda gwamnan Anambra, Farfesa Charles Soludo, ya fito, ya shiga hannun masu garkuwa ne a garin Aguata ranar Lahadi.

Kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Anambra, DSP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN).

Kara karanta wannan

Sokoto: Wani Malami ya yi alkawarin daukar nauyin iyayen ɗalibar da ta zagi Annabi, yace sun gama wahala a duniya

An sace ɗan majalisa a Anambra.
Yan bindiga sun sace Ɗan majalisar jiha a yankin mazaɓar Gwamnan Anambra Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

Premium Times ta ruwaito cewa an gano motar da ɗan majalisar ke ciki yayin da lamarin ya faru Siena SUV, a cewar hukumar yan sanda.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wane mataki hukumar yan sanda ta ɗauka?

Kakakin yan sandan, Mista Ikenga, ya ce tuni jami'an yan sanda suka bazama neman masu garkuwan da kuma kubutar da ɗan majalisar cikin koshin lafiya.

Haka nan kuma ya tabbatar da kashe mamban ƙungiyar yan Bijilanti, wanda ke kan Babur a garin Oko, jihar Anambra duk a ranar Lahadi.

Ikenga ya ƙara da cewa ɗan Bijilantin da aka kashe na sanye da kayan jami'an tsaro na musamman, amma ba jami'in hukumar yan sanda ba ne.

Ya kuma ƙaryata rahoton da mutane ke yaɗa wa a kafafen sada zumunta cewa mamacin ɗan sanda ne, inda ya roki al'umma su yi watsi da rahoton.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: Yan bindiga sun banka wuta a Kamfanin rarraba wutar lantarki, sun tafka ɓarna

Punch ta rahoto Ya ce:

"A ranar 15 ga watan Mayu, jami'an hukumar yan sandan jihar Anambra sun gano wata gawa sanye da rigar yan sanda a kan babbar hanyar Oko, kuma bincike ya nuna ba mamba bane a hukumar yan sanda."
"Hukumar yan sanda ta fara bincike don gano ainihin bayanan mamacin tare da gano musabbabin da ya haddasa mutuwarsa."

A wani labarin kuma Iyayen Ɗalibar da ta zagi Annabi a Sokoto sun yi magana kan kashe ɗiyarsu bayan binne gawarta

Iyayen ɗalibar da ta yi kalaman Batanci ga Annabi Muhammad (SAW) sun yi magana kan abinda ya faru a Sakkawato bayan binne gawarta.

Mahaifin Debora Samuel ya bayyana yadda direbobi suka guje shi kafin ya sami wanda ya ɗakko gawar zuwa Neja kan N120,000.

Asali: Legit.ng

Online view pixel