'Batanci: Bayan Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Deborah a Sokoto, Osinbajo Ya Yi Magana Da Kakkausar Murya

'Batanci: Bayan Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Deborah a Sokoto, Osinbajo Ya Yi Magana Da Kakkausar Murya

  • Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Yemi Osinbajo ya kwatanta kisan dalibar aji biyu ta Kwalejin Ilimin Shehu Shagari, Deborah Samuel bisa zarginta da batanci, a matsayin abu mai ban takaici
  • Osinbajo ya bayyana hakan ne ga manema labarai a ranar Juma’a a wurin jirgin shugaban kasa cikin filn jirgin Nnamdi Azikwe da ke Abuja bayan dawowarsa daga Uyo, Jihar Akwa Ibom
  • Mataimakin shugaban kasar ya yaba wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari da Sarkin Musulmi akan yadda su ka fito su ka yi alawadai akan kisan nata da matasan su ka yi

Abuja - Yemi Osinbajo, Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya ya yi alawadai da kisan Deborah Samuel, dalibar aji biyu ta Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sokoto bisa zarginta da batanci, rahoton The Guardian.

Kara karanta wannan

'Batanci: Atiku Ya Ce Ba Shine Ya Wallafa Rubutun Sukar Kashe Ɗalibar Sokoto a Shafinsa Ba

Ya nuna alhininsa ne yayin tattaunawa da manema labarai a ranar Juma’a a bangaren jirgin shugaban kasa da ke filin jirgin Nnamdi Azikwe a Abuja, bayan dawowarsa daga Uyo, Jihar Akwa Ibom.

'Batanci: Bayan Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Deborah a Sokoto, Osinbajo Shi Ma Ya Magantu
Kisan Deborah a Sokoto abin damuwa ne matuka ga zuciya, In Ji Osinbajo. Hoto: The Punch.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana jin dadinsa akan yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari da Sultan din Sokoto su ka nuna rashin jindadinsu akan lamarin.

Ya yaba wa shugaban kasa da Sarkin musulmi akan alawadan da su ka yi

Kamar yadda The Punch ta ruwaito, ya kada baki inda ya ce:

“Bari in fara da cewa, shugaban kasa ya nuna rashin jin dadinsa akan aukuwar wannan lamarin ta wata takarda wacce ya saki.
“Zan iya cewa abin akwai ban takaici, tare da taba zuciya, irin wannan kisan wulakanci da matasa su ka yi bayan daukar doka a hannunsu; gaskiya wannan abu be yi dadi ba.

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

“Yadda gwamnatin Jihar Sokoto da Sultan su ka nuna bacin ransu ma sun kyauta kwarai. Ina kyautata zaton nuna bacin ransu da su ka yi da sauran miliyoyin ‘yan Najeriya ma ya nuna rashin dacewar aika-aikar. Kuma muna fatan za a yi gaggawar hukunta wadanda su ka halaka ta.”

Ya nuna tsananin damuwarsa akan halin da iyayen yarinyar su ka shiga bayan jin batun mutuwarta

Osinbajo ya kwatanta rashin dacewar yadda matasan su ka dauki doka a hannunsu kasancewar akwai hukumar da ya dace a kai wa kara.

Ya mika ta’aziyyarsa ga ‘yan uwan mamaciyar tare da fatan Ubangiji ya ba su hakuri.

Ya ci gaba da cewa:

“Ina tunanin irin tashin hankalin da ‘yan uwanta su ka shiga bayan samun labarin mutuwarta da kuma aika-aikar da aka yi mata.
“Hakika abin akwai taba zuciya. Mu na yi musu ta’aziyyar tare da fatan Ubangiji ya sanya musu salama a zuciyoyinsu."

Kara karanta wannan

Sarkin Bauchi ya yi maza ya yi karin-haske, ya karyata jita-jitar goyon bayan Osinbajo

'Batanci: Atiku Ya Ce Ba Shine Ya Wallafa Rubutun Sukar Kashe Ɗalibar Sokoto a Shafinsa Ba

A wani rahoton, Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP ya nisanta kansa daga yin ala-wadai akan kisan Deborah Samuel.

Deborah dalibar aji biyu ce a kwalejin ilimi ta Shehu Shagari da ke Jihar Sokoto, kuma kirista ce, an halaka ta ne bisa zarginta da yin batanci ga Annabi Muhammad SAW.

Sai dai Atiku ya yi wata wallafa a Twitter inda ya ce:

“Babu adalci dangane da kisan muguntar da aka yi mata. An halaka Deborah Yakubu kuma wajibi ne a kwatar mata hakkinta akan wadanda su ka halaka ta. Ina mai yi wa ‘yan uwanta da kawayenta ta’aziyya.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164