Lauya ya kwashe kudin dake akawunt din dan sanda bayan ya mutu, EFCC ta damkeshi

Lauya ya kwashe kudin dake akawunt din dan sanda bayan ya mutu, EFCC ta damkeshi

  • Lauyan wani jami'in dan sanda CSP ya kwashe kudin dake asusun kwastomansa bayan da ya mutu
  • Lauyan ya hada baki da wasu mutane wajen wawure kimanin milyan goma sha hudu
  • Matar dan sanda tayi gaggawa kai kara wajen yan sanda an kwashe mata kudin gadon da mijinta ta bari

Uyo - Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC ta damke lauya da wasu mutum shida kan satan kudin dan sandan da ya mutu.

EFCC ta gurfanar da lauyan da abokansa gaban babban kotun tarayya dake Uyo, jihar Akwa Ibom.

Hukumar ta bayyana hakan a jawabin da ta saki ranar Juma'a a shafinta na yanar gizo.

A cewarta, matar dan sandan ta shigar da kara kan yadda suka kwashe kudi milyan 13 dake asusun dan sanda wanda babban sufritanda ne kafin mutuwarsa.

Kara karanta wannan

Dokar kulle: Bishop Kukah ya yabawa matakin Tambuwal, ya karyata batun kai hari gidansa

EFCC ta damkeshi
Lauya ya kwashe kudin dake akawunt din dan sanda bayan ya mutu, EFCC ta damkeshi Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar jawabin:

"Sashen EFCC na Uyo ta gurfanar da da Barista Samuel Ebitu tare da mutum shida, kan laifin sace N13,171,415.25 daga asusun bankin mataccen dan sanda."
"An gurfanar da su gaban Alkali Agatha Okeke."
"Sauran mutum shidan sun hada da Etimbuk Godwin Edet, Michael Jeremiah Isong, Sunny Isong, Godwin Ekanem, Emmanuel Jackson Isong da Harrison Ofuomah Emamoke.

Hukumar ta kara da cewa matar marigayin ce ta shigar da kara kan yadda suka wawure kudin gadon da mijinta ya bari.

Jonathan ya kawo shawarar karkatar da N2bn domin neman tazarce – Tsohon Gwamna

A wani labarin kuwa, hukumar EFCC ta koma kotu da tsohon gwamnan jihar Neja, Dr. Muazu Babangida Aliyu da kuma wasu mutane biyu; Tanko Beji da Umar Nasko.

EFCC ta bada wannan sanarwa a shafinta na Facebook a ranar Alhamis, 12 ga watan Mayu 2022.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun kashe mutum 1, sun yi garkuwa da wasu 20 a Kaduna

Kamar yadda mu ka ji labari, shari’ar Muazu Babangida Aliyu da sauran wadanda ake tuhuma sun je gaban Alkali Mikail Aliyu na babban kotun jihar Neja.

A zaman da aka yi na ranar Alhamis a kotun da ke zama a garin Minna, hukumar EFCC ta kira Bala Mohammed domin gabatar da shaida gaban Alkali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel