EFCC: Jonathan ya kawo shawarar karkatar da N2bn domin neman tazarce – Tsohon Gwamna

EFCC: Jonathan ya kawo shawarar karkatar da N2bn domin neman tazarce – Tsohon Gwamna

  • Hukumar EFCC ta na shari’a da su Dr. Muazu Babangida Aliyu, an koma zaman kotu a makon nan
  • Lauyoyin EFCC su na zargin tsohon gwamnan na jihar Neja da wasu hadimansa ne da satar N2bn
  • Dr. Babangida Aliyu ya fadawa jami’an EFCC cewa Goodluck Jonathan ya ce a kashe kudin a zabe

Niger - Hukumar EFCC ta koma kotu da tsohon gwamnan jihar Neja, Dr. Muazu Babangida Aliyu da kuma wasu mutane biyu; Tanko Beji da Umar Nasko.

EFCC ta bada wannan sanarwa a shafinta na Facebook a ranar Alhamis, 12 ga watan Mayu 2022.

Kamar yadda mu ka ji labari, shari’ar Muazu Babangida Aliyu da sauran wadanda ake tuhuma sun je gaban Alkali Mikail Aliyu na babban kotun jihar Neja.

Kara karanta wannan

Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

A zaman da aka yi na ranar Alhamis a kotun da ke zama a garin Minna, hukumar EFCC ta kira Bala Mohammed domin gabatar da shaida gaban Alkali.

Bala Muhammed shi ne mutum na 11 da ya tsaya a matsayin shaidan da EFCC ta dogara da shi a shari’ar da ake yi da tsohon gwamnan a kan satar kudi.

Lauyoyin EFCC su na zargin cewa tsohon gwamna Aliyu da wadannan mutane da ake shari’a da su, sun karkatar da N2bn da aka ware domin yin ayyuka.

Muazu Babangida Aliyu da Goodluck Jonathan
Dr. Muazu Babangida Aliyu da Dr. Goodluck Jonathan Hoto: Getty Images /NAIJ
Asali: UGC

Gwamnatin tarayya ta fitar da kudin ne da nufin aiwatar da ayyukan da za su taimaka a magance matsalolin yanayi da ake fama da su a jihohin Arewa.

Ashe shawarar Jonathan ce

Jaridar Politics Digest ta ce Babangida Aliyu ya shaidawa hukuma cewa Goodluck Jonathan ya kawo shawarar a karkatar da kudin domin lashe zabe a 2011.

Kara karanta wannan

Boko Haram sun sheke na kusa da Shekau bayan yunkurin mika kansa ga sojoji

Mai magana da yawun bakin EFCC, Wilson Uwujaren, ya ce mutum na farko da ake tuhuma, ya sanar da jami’an hukumar yadda aka yi da wadannan kudi.

Da aka yi hira da Babangida Aliyu, ya ce daga tattaunawarsa da shugaban Najeriya na lokacin ya samu damar amfani da dukiyar jihar domin lashe zaben 2011.

Za a cigaba da shari'a

Bala Mohammed ya tabbatar cewa kudin sun tafi ne wajen yakin neman zabe, sannan ya nemi kotu ta ba shi lokaci domin ya shiryawa zaman da za ayi da kyau.

Lauyan gwamnati da ya shigar da kara, Faruk Abdallah bai yi na'am da wannan roko ba. A karshe dai Mai shari’a Aliyu ya daga zama, za a koma kotu a yau Juma’a.

Ana binciken PDP da APC

Kun samu rahoto hukumar yaki da rashin gaskiya ta na zargin cewa jam’iyyun PDP da na APC sun saba dokar EFCC ta 2021 da sabuwar dokar safarar kudi.

Kara karanta wannan

Yajin aikin ASUU: Daliban jami'a sun fusata, sun ba lakcarori da gwamnati wa'adi su bude jami'o'i

Yanzu haka EFCC ta na binciken asusun jam’iyyun, ta bukaci bankuna su kawo mata takardar bude akawun da bayanin kudin da suka shiga asusun a 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel