Mafi girman laifi ta yi: Farfesa Maqari ya goyi bayan kashe dalibar da ta zagi Annabi

Mafi girman laifi ta yi: Farfesa Maqari ya goyi bayan kashe dalibar da ta zagi Annabi

  • Shahararren malamin addinin Islama kuma limamin babban masallacin Abuja ya yi martani kan kisan wata daliba a Sokoto
  • Malamin ya nuna matukar shiga tashin hankali da jin yadda dalibar ta zagi janabin manzon Allah SAW
  • Hakazalika, ya yi martani ga mutanen da ke sukar musulmai saboda daukar matakin kashe dalibar a bainar jama'a

Abuja - Babban limamin masallacin Abuja, Farfesa Ibrahim Maqari ya bayyana rashin jin dadinsa ga yadda wata daliba ta shararawa Annabin Allah ashariya a wani faifan sauti da ya yadu a yanar gizo.

A bangare guda, malamin na addinin Islama ya amince da daukar doka a hannu ba daidai bane, amma ya nuna goyon bayansa ga hakan idan dai janibin manzon Allah aka taba.

Farfesa Maqari ya goyi bayan kashe dalibar da ta zagi Annabi
Mataki muka dauka: Farfesa Maqari ya goyi bayan kashe dalibar da ta zagi Annabi | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

A wasu rubuce-rubuce da ya yada a shafinsa na Twitter, malamin ya nuna fushi tare shiga tashin hankali bisa jin yadda aka ci mutuncin zababben Allah Annabi Muhammadu SAW.

Kara karanta wannan

'Batanci: Bayan Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Deborah a Sokoto, Osinbajo Ya Yi Magana Da Kakkausar Murya

Ya yada wani hoto mai dauke da rubutu yana cewa:

"Daukan doka a hannu laifi ne. Amma dan karamin laifi ne idan aka hada shi da zagin janabin Shugaba SallalLahu AlaiHi wa AliHI wa sallam.
"Ba mu da karfin zuciyar da zamu iya shagala da karamin laifi mu bar mafi girman laifuka."

Hakazalika ga mabiyansa masu magana da harshen Turancin Ingilishi, malamin na darikar Tijjaniya ya bayyana sakonsa gare su, ga fassarar abin da ya rubuta cikin harshen Turancin:

"Ya kamata kowa ya sani cewa mu mMusulmi muna da wasu jajayen layukan da DOLE ba za a ketare su. Janabin Annabi (SAW) shi ne kan gaba a cikin jajayen layukan. Idan har ba a magance koke-kokenmu yadda ya kamata ba, to bai kamata a rika sukar mu ba don mun magance da kanmu."

Kara karanta wannan

Karin bayani: Tambuwal ya gana da malaman Islama kan batun dalibar da ta zagi Annabi

Bishop Kukah ya yi martani kan kashe dalibar da ta yi batanci ga Annabi

A wani labarin, Babban Limamin Cocin Katolika na Diocese na Sokoto, Mathew Kukah, ya yi Allah-wadai da kisan wata dalibar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sokoto a yau Alhamis.

Ya kuma yi kira da a kwantar da hankali kan lamarin, yana mai cewa lamarin ba na addini bane, inji rahoton Channels Tv.

A cewar rundunar ‘yan sanda, an zargi Deborah Samuel, ‘yar matakin karatu na biyu, da yin wani rubutu a dandalin sada zumunta na yanar gizo wanda ya nuna alamun batanci ga manzon Allah (SAW).

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.