An yi ram da mai mulki a Kaduna yana dauke da AK-47 kusa da sansanin ‘Yan bindiga

An yi ram da mai mulki a Kaduna yana dauke da AK-47 kusa da sansanin ‘Yan bindiga

  • Jami’an tsaro sun kama wani mutumi yana rike da bindiga a yankin dajin Galadimawa a Kaduna
  • Bincike ya nuna wannan Bawan Allah da aka cafke yana kan kujerar Kansila ne yanzu a garin Soba
  • Ana tunanin har zuwa yanzu Hon. Abdul Adamu Kinkiba yana tsare a hedikwatar ‘Yan Sanda a Kaduna

Kaduna - Jami’an tsaron da ke aiki a yankin Galadimiwa, karamar hukumar Giwa, jihar Kaduna sun yi ram da wani Bawan Allahi, Abdul Adamu Kinkiba.

Daily Trust ta ce Hon. Abdul Adamu Kinkiba Kansila ne a karamar hukumar Soba da ke jihar.

Honarabul Abdul Adamu Kinkiba ya fada hannun jami’an tsaron ne a kusa da wani sanannen gungu da ‘yan bindiga su ke fakewa, su na addabar mutane.

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa Kansilan yana rike da wannan bindiga ta AK-47 ne a kan babur, a lokacin da wasu dakarun tsaro suka ci karo da shi.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

Da ake yi masa tambayoyi, Abdul Kinkiba ya shaidawa jami’an tsaron cewa wani mutum ne ya ba shi bindigar, amma ya ce ba zai iya tuna sunan mutumin ba.

Yadda abin ya faru - Majiya

“Ya ce an fada masa cewa bindigar ta tawagar wani ce. A cewarsa, an fada masa ya zo ya tsaya da zarar an wuce gadar da ke daf da dajin Galadimawa.”
Wannan wuri ne da miyagun ‘yan bindiga suke samun mafaka, an fada masa cewa wani mutum zai zo nan ya karbi bindigar daga hannunsa.” – Majiya.
Kaduna
Taron jami'an tsaro a Kaduna Hoto: @GovKaduna
Asali: Twitter

Kansilanmu ne inji Soba LG

Shugaban karamar hukumar Soba, Honarabul Suleiman Yahaya Richifa ya tabbatar da wannan labari, ya ce babu shakka wanda aka kama Kansila ne a garinsu.

Injiniya Suleiman Yahaya Richifa ya ce Abdul Kinkiba shi ne Kansilan gundumar Kinkiba a Soba.

Kara karanta wannan

Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

Amma Richifa ya ki cewa uffan bayan hakan, ya nuna samun wannan labarin ya matukar girgiza shi, ya ce ba zai iya magana a kan rahoton a halin da ake ciki ba.

Kawo yanzu, an wuce da wannan mutumi zuwa babbar hedikwatar ‘yan sanda da ke garin Kaduna, domin amsa tambayoyi inda za a binciki lamarin da kyau.

Tinubu ya zo Kaduna

Idan aka koma siyasa, za a ji labari yau ne Bola Tinubu ya hadu da Nasiru El-Rufai. Ba tare da wani boye-boye ba, Gwamnan ya nuna masa duk su na tare da shi.

Kwanakin baya da Tinubu ya zo ta’aziyya a jihar Kaduna bayan an dauke mutane a jirgin kasa, Malam El-Rufai bai nuna zai goyi bayan takarar Tinubu a APC ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng