Shirin 2023: Hukumar zabe ta INEC ta fadi sabon wa'adin rajistar katin zabe

Shirin 2023: Hukumar zabe ta INEC ta fadi sabon wa'adin rajistar katin zabe

  • Gabanin gudanar da zaben fidda gwani na jam'iyyun siyasa a kasar, hukumar zabe ta INEC ta bayyana cewa za ta dakatar da aikin rajistar masu kada kuri'a ta yanar gizo
  • Hukumar zaben kasar ta bayyana cewa matakin ya zama wajibi ga hukumar domin duba rajistar da kuma kara kammala rajista kafin ranar 30 ga watan Yuni
  • Mahmood Yakubu, shugaban hukumar ta INEC, ya bayyana cewa, wannan atisayen zai baiwa hukumar zabe damar tsaftace bayanan rijistar kafin zaben 2023 mai zuwa

Abuja - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce za ta dakatar da aikin rajistar kada kuri’a ta yanar gizo a ranar 30 ga watan Mayu, TheCable ta ruwaito.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC a baya ta ce za a ci gaba da gudanar da rijistar ta yanar gizo da kuma a ofishi a lokaci guda har sai an dakatar da aikin CVR a ranar 30 ga Yuni, 2022.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Saraki ya bayyana alherin da ya tanadar wa 'yan Najeriya idan ya gaji Buhari

Rajistar katin zabe zai kawo karshe a karshen Mayu
Shirin 2023: Hukumar zabe ta INEC ta fadi sabon wa'adin rajistar katin zabe | Hoto: thecable.ng
Asali: Depositphotos

Amma da yake magana a ranar Laraba a taro karo na biyu na watanni uku da kungiyoyin farar hula na 2022, Mahmood Yakubu, shugaban INEC, ya ce za a kawo karshen yin rijistar ta yanar gizo a watan Mayu.

Ya ce hakan zai bai wa wadanda suka yi rajista ta yanar gizo lokaci domin su kammala rajistarsu a ofishi kuma zai ba hukumar damar tsaftace bayanan rajistar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

"Kamar yadda kuka sani, rijistar masu kada kuri'a (CVR) da ke ci gaba da gudana zai zo karshe a wata mai zuwa watau 30th June 2022. Duka rijista ta yanar gizo da kuma rajista a cibiyoyin da aka kebe suna gudana lokaci guda."

Shugaban INEC ya musanta raɗe-raɗin yana shirin tsayawa takarar shugaban kasa a 2023

Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, ya musanta rahoton dake yawo cewa da yuwuwar ya nemi takarar shugaban ƙasa a 2023.

Kara karanta wannan

Ta kanmu mu ke, ba ta kashe N100m ba: Fulani sun musanta sayen fom ga Jonathan

Ƙungiyar marubutan ƙare haƙƙin ɗan adam ta Najeriya, a ranar Lahadi, ta yi kira ga yan Najeriya ka da su kaɗu idan suka ga shugaban INEC ya sayi Fom ɗin APC miliyan N100m.

Jaridar Punch ta rahoto cewa ƙungiyar ta yi wannan tunani ne bayan ganin an saya wa gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, Fom ɗin nuna sha'awa da tsayawa takara a APC.

Amma da yake martani ta hannun Sakataren watsa labaransa, Rotimi Oyekanmi, ranar Lahadi, shugaban INEC ya bayyana cewa ba shi da sha'awar shiga tseren takarar kujera lamba ɗaya a Najeriya.

A sanarwar da sakataren ya fitar don musanta jita-jitar mai taken, "Kiran da ake shugaban INEC ya shiga tseren takara a 2023," Yakubu ya ce hakan ba zai taɓa yuwuwa ba.

Ba za a tsawaita wa'adin zaben fidda gwani ba – INEC ga jam’iyyun siyasa

A wani labarin, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ce wa’adin da aka kayyade don gudanar da zaben fidda gwani na nan daram a kan Juma’a, 3 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

2023: Jam’iyyun siyasa sun bukaci a sauya jadawalin zabe, INEC ta yi martani

Hukumar zaben ta ce jam’iyyun siyasa na da sauran wata daya cif daga yau domin kammala zaben fidda gwaninsu, jaridar The Cable ta rahoto.

A cikin wata sanarwa da ta saki a ranar Alhamis, 5 ga watan Mayu, INEC ta ce an baiwa dukkanin jam’iyyun siyasa guda 18 sanarwar da yakamata wanda ke nuna ranakun gudanar da babban taronsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.