Boko Haram sun sheke na kusa da Shekau bayan yunkurin mika kansa ga sojoji
- Rahotannin da ke iso mu sun nuni da cewa, 'yan ta'addan ISWAP sun hallaka kwamandan Shekau a cikin dajin Sambisa
- Wannan na zuwa ne bayan da 'yan ta'addan suka gano yana shirin tuba tare da mika kansa ga sojojin Najeriya
- A baya dai wannan jigon kusa da Shekau ya hada kai da ISWAP ne bayan da shugabansu Shekau ya mutu
Borno - Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan ta’addar Boko Haram da ISWAP sun kawar da daya daga cikin manyan kwamandojin su Abu-Sadiq wanda aka fi sani da Burbur bisa zarginsa da shirin mika wuya ga dakarun gwamnati.
Jaridar Leadership ta tattaro cewa an kashe Burbur ne a kauyen Galta da ke kusa da Madagali bayan tuhumarsa da laifin cin amana a wata kotun 'yan ta'adda ta Ya-Shaik, ISWAP Fiye na dajin Sambisa.
A cewar wani rahoton sirri da aka samu daga majiyar soji ta bayyana cewa, Bubur ya kasance a gidan yari na ISWAP a watan Afrilu bayan da aka kama shi hannu dumu-dumu yana shirin mika kansa ga soji. A karshe an kashe shi a ranar 9 ga Mayu, 2022.
Batun na fitowa ne daga kwararre kan harkar yaki da tsaro Zagazola Makama a birnin Maiduguri.
Abubuwan da ya kamata ku sani game da Burbur
Majiyar ta ce kafin rasuwarsa, Burbur ya kasance mataimakin shugaban tsageru, mai kula da dajin Sambisa da kusurwowi uku na Timbuktu.
An nada shi ne a watan Mayun 2021 lokacin da ya yi mubaya'a ga ISWAP, saboda saninsa sosai game da yankin da kuma dabarunsa na baya a matsayin kwamandan ayyukan ta'addanci a mafakar marigayi Abubakar Shekau.
Burbur ya kasance mai kula da kai hare-hare a sansanonin sojoji da garuruwa da suka hada da Michika, Madagali, Askira Uba da sauran sassan jihar Adamawa.
A matsayinsa na daya daga cikin amintattun mashekin dan ta'adda marigayi Abubakar Shekau, an sha ganin Bubur na tsaye a baya da fagen Shekau a cikin faya-fayan bidiyo.
Sauran manyan kwamandojin Shekau da suka yi mubaya’a ga ISWAP sun hada da Ba’a Umara, Ba’ana Biga, Abu Maryam, Abu Ayuba, da Ibn Yusuf.
Sama da tubabbun 'yan ta'adda 51,000 da iyalansu ke hannunmu, Rundunar sojin Najeriya
Fiye da tubabbun 'yan ta'adda 51,000 da iyalansu ne suka zub da makamansu ga sojojin yankin Arewa maso Gabas kamar yadda sojojin suka bayyana.
Kwamandan rundunar operation Hadin Kai, Manjo Janar Chris Musa, ya bayyana wa Channels TV yayin tattaunawar da suka yi da shi a ranar Litinin.
Ya bayyana yadda mazauna yankin suka dinga taimakon sojoji, musamman yadda suka samu bayanan sirri duk da cewa akwai bangaren da aka sanya wa shamakin sadarwa.
Ya ce:
"Muna samun bayanai da zarar abubuwa sun faru.
"Wani lokacin, kalubalen da muke fuskanta shi ne hanyar sadarwa kasancewar ba ko ina bane ake samun kafar sadarwar ba; amma da zarar sun isa inda za su iya tuntubar mu suna tura mana sako.
Borno: Sojin Najeriya sun bindige 'yan ISWAP 22, sun kwato makamai a tafkin Chadi
A wani labari na daban, dakarun jami'an tsaron hadin guiwa na kasashe (MNJTF) sun sheke 'yan Boko Haram 22 ko 'yan ta'addan ISWAP yayin da suke cin karensu ba babbaka a tafkin Chadi.
Babban kakakin rundunar MNJTF a N'Djamena na Chadi, Kamarudeen Adegoke ne ya tabbatar da hakan a wata takarda da ta fita ranar Lahadi, Premium Times ta ruwaito.
Adegoke, laftanal kanal, ya ce an sheke 'yan ta'adda a Tumbun Rabo cikin karamar hukumar Abadam a ranar 27 ga watan Afirilu.
Asali: Legit.ng