Jirgin ƙasa ya yi ciki da wata Motar Bas makare da Fasinjoji bayan Direba ya ƙi jin shawara

Jirgin ƙasa ya yi ciki da wata Motar Bas makare da Fasinjoji bayan Direba ya ƙi jin shawara

  • Jirgin kasa ya kaɗe wata Motar Bas ta haya ɗauke da Fasinjoji yayin da ya zo wucewa a Ilupeju bye-pass jihar Legas
  • Rahoto ya nuna cewa Direban Motar ne ya ki bin umarnin jami'an ba da hannu, Fasinjojin Motar sun yi kokarin direwa daga ciki
  • Babu fasinjan da ya rasa rayuwarsa a cewar hukumar LASEMA, amma biyu suna kwance a Asibiti

Lagos - Wasu Fasinjoji sun jikkata wasu kuma suka tsallake rijiya da baya bayan wani Jirgin ƙasa ya yi ciki da wata Motar Bus ta haya a jihar Legas, kamar yadda Tribune Online ta rahoto.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan Direban Motar ya yi kunnen uwar shegu da gargaɗin mutane na ya jinkirta Jirgin da ya kusanto ya wuce.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

Lamarin ya faru ranar Talata a kan layin dogo da ya ratsa ta hanyar Ilupeju bye-pass lokacin da Direban Bus Toyota Hiace ya ƙi dakata wa bayan jami'an ba da hannu sun umarci Motoci su tsaya jirgi ya wuce.

Hatsarin Jirgin ƙasa da Bas.
Jirgin ƙasa ya yi ciki da wata Motar Bas makare da Fasinjoji bayan Direba ya ƙi jin shawara Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

A cewar jami'an ba da agajin gaggawa LASEMA ta jihar Legas, waɗan da suka yi saurin zuwa wurin bayan samun rahoto, bisa tilas Fasinjojin suka fice daga Motar.

A cewar hukumar LASEMA, duk da haka mutum biyu sun jikkata yayin kokarin tsira da rayuwarsu, an ba su taimakon gaggawa daga bisani aka kai su babban Asibitin yankin.

LASEMA ta ce:

"Ɗaukin da jami'an mu suka kai cikin lokaci ne ya daƙile munin lamarin wanda ka iya sanadin rasa rayuka a Ilupeju bye-pass ranar 10 ga Watan Mayu, 2022."

Kara karanta wannan

Cikakken Labari: Wani Bam Ya Tashi a Masallaci Yayin da Mutane ke tsaka da Sallar Jumu'a

"Lokacin da jami'ai suka isa sun gano wata Motar Bas mai lamabar rijista EKY 888 XW da Jirgin kasa ne suka haɗe. Rashin kulawa da gangancin direban Bas ne ya jawo hatsarin."
"Bayanan da muka samu sun nuna cewa an dakatar da Direban lokacin da zai ratsa amma ya yi kunnen uwar shegu da umarnin jami'an ba da hannu da ke aiki a wurin."

Shin akwai wanda ya rasa rayuwarsa?

Hukumar LASEMA ta ƙara da cewa bisa sa'a babu wanda ya rasa rayuwarsa sanadiyyar hatsarin, sai mutum biyu da suka ji raunuka kuma ana kula da lafiyarsu.

A wani labarin kuma Wani abun fashewa da ake zaton Bam ne ya tashi a sansanin Sojojin Najeriya da ke Jalingo a Taraba

Sai dai wannan karon, bayanai sun nuna cewa fashewar ta auku ne a kusa da Hedkwatar sojoji amma babu wanda ya rasa rayuwarsa.

Kakakin hukumar yan sanda na jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin, wanda ya auku da daren Talata.

Kara karanta wannan

Gara ku biya kuɗin fansar Fasinjojin jirgin kasa da ku sayi Fom ɗin takara a 2023, Sheikh Gumi

Asali: Legit.ng

Online view pixel