Kano: Kotu tan yanke wa matashi mai shekaru 19 hukuncin kisa ta hanyar rataya

Kano: Kotu tan yanke wa matashi mai shekaru 19 hukuncin kisa ta hanyar rataya

  • Babbar kotun jihar Kano karkashin jagorancin alkali Usman Na'abba ta yanke wa matashi mai shekaru 19 hukuncin kisa
  • Kamar yadda alkalin ya bayyana, shaidu masu yanke hanzari da uziri sun tabbatar da cewa matashin ya sace kuma ya halaka 'dan yayar shi
  • A 2019, Ibrahim Khalil ya sace Ahmad Ado mai shekaru 5 daga kwatas din Karkasara kuma ya manne masa hanci da baki da salatif

Kano - Wata babbar kotu da ke Kano a ranar Litinin ta yanke wa wani Ibrahim Khalil mai shekaru 19 hukuncin kisa ta hanyar rataya kan garkuwa da dan yayar shi mai shekaru biyar mai suna Ahmad Ado da kuma zama silar mutuwarsa da yayi.

Khalil, wanda ba a bayyana adireshinsa ba, an yanke masa hukuncin laifuka biyu da suka hada da garkuwa da mutane da kisan kai ta hanyar mannewa yaro hanci da baki da salataf, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya rigamu gidan gaskiya

Kano: Kotu tan yanke wa matashi mai shekaru 19 hukuncin kisa ta hanyar rataya
Kano: Kotu tan yanke wa matashi mai shekaru 19 hukuncin kisa ta hanyar rataya. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: Facebook

Alkali Usman Na'abba, ya tsaya kan cewa masu gabatar da kara sun tabbatar da zargin da suke cike da dalilai masu yanke hanzari kuma ya yanke wa wanda aka kama da laifin garkuwa da mutanen hukuncin shekaru 14 a gidan maza.

Na'abba ya kara da yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kama shi da laifin kisan kai da aka yi.

Tun farko, lauyan masu gurfanarwa, Lamido Sorondinki, ya sanar da kotu cewa wanda aka yanke wa hukuncin ya aikata laifin a 2019 a kwatas din Karkasara da ke Kano.

"Wanda ke kare kansan ya yi garkuwa da 'dan yayarsa, Ado kuma a hakan ne ya sanya salatif tare da toshe masa hanci da baki wanda hakan ya kawo ajalinsa.
"Ya birne shi a kabari mara zurfi a Sabuwar Sheka da ke Kano," yace.

Kara karanta wannan

Sokoto: Bishop Kukah ya yi martani kan kashe dalibar da ta yi batanci ga Annabi

Masu kara sun kawo shaidu uku gaban kotu da kuma abubuwan shaida hudu domin tabbatar wa da kotun. Wanda aka yanke wa hukuncin ya musanta aikata laifin da ake zarginsa da shi.

Kamar yadda mai gabatar da kara yace, laifin ya ci karo da tanadin sashi na 274 da 221 na Penal Code .

Hanifa: Abdulmalik Tanko ya yarda da sace ta, ya karyata batun kashe yarinyar

A wani labari na daban, Abdulmalik Tanko, malamin makaranta da ake zargi da sace dalibarsa mai shekaru 5, Hanifa Abubakar, da kuma ya kashe ta, ya sake musanta batun sanin yadda aka yi yarinyar ta mutu.

Ya karyata batun ne a babbar kotu mai lamba ta 5, da ke zama a Audu Bako a ranar Litinin, 9 ga watan Mayu, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Tanko, wanda a baya ya amince da hada baki da wasu wajen aikata laifin, ya musanta sauran tuhume-tuhume uku da ake masa da su da suka hada da yin garkuwa da yarinyar da kuma kashe ta daga baya.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Buhari Ya Roƙi ASUU Ta Janye Yajin Aiki, Ya Ba Wa Ɗalibai Haƙuri

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng