Jerin yadda aka kashe yan sanda uku, Sojoji biyu da wasu mutum 73 cikin mako ɗaya a Najeriya

Jerin yadda aka kashe yan sanda uku, Sojoji biyu da wasu mutum 73 cikin mako ɗaya a Najeriya

  • Bayanan da aka tattara sun nuna cewa a makon da ya gabata aƙalla mutum 78 suka rasa rayukansu a faɗin Najeriya
  • Yan sanda uku, Sojoji biyu da mutane 73 ne yan ta'adda suka kashe, adadin ya karu fiye da na makon da ya gabaci wannan
  • Daga ciki har da harin da yan bindiga suka kai yankunan kananan hukumomi biyu a Zamfara, wanda ya yi ajalin mutum 56

Kashe-kashe a Najeriya ya ƙaru a makon da ya gabata (1 ga watan Mayu zuwa 7 ga watan Mayu) inda aƙalla mutum 78 suka rasa rayukan su a sassan ƙasar nan.

Adadin ya karu idan aka kwatanta da na wancan makon da ya gabaci wannan, inda aƙalla mutun 15 suka rasa rayukan su, cikinsu har da Soja ɗaya.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

Premium Times ta tattara wannan adadin ne daga rahotannin da kafafen watsa labarai suka buga. Dukkan waɗan da ba'a rahoto ba, ba su shiga cikin adadin ba.

Daga cikin yawan waɗan da suka rasa rayukna su, mutum 5 jami'an tsaro ne da suka haɗa da yan sanda uku da Sojoji biyu, sauran 73 kuma sun kasance fararen hula.

Matsalar tsaro a Najeriya.
Jerin yadda aka kashe yan sanda uku, Sojoji biyu da wasu mutum 73 cikin mako ɗaya a Najeriya Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Jerin yadda lamarin ya faru

Kudu maso gabashin Najeriya

A ranar Lahadi wasu yan bindiga suka yanka Sojoji biyu a wani wuri da ba'a gano ba a jihar Imo. Sojojin da abun ya shafa, Sajan A. M. Linus da Matarsa da ba'a gano bayananta ba, an gutsire musu kawuna bayan harbe su da bindiga har lahira.

Wasu mambobi biyu da ake zargin yan kunyiyar awaren IPOB ne da ESN sun sheka barzahu yayin gwabzawa da dakarun yan sanda a Agwa, ƙaramar hukumar Oguta, jihar Imo.

Kara karanta wannan

Cikakken Labari: Wani Bam Ya Tashi a Masallaci Yayin da Mutane ke tsaka da Sallar Jumu'a

Waɗan da ake zargin sun fito daga wasu dazuka da ke kewaye kuma suka buɗe wa Motar yan sanda dake aikin Sintiri wuta, hakan ya yi sanadun mutuwar ɗan sanda ɗaya.

A jihar Ebonyi kuma, wata tawagar masu fyaɗe sun halaka wata matashiya yar shekara 26, Ugochukwu Nworie, a Otal din Hope-in kan layin Nine Ngbowo, babban birnin Ebonyi ranar Litinin.

Haka nan a jihar Anambra, yan bindiga sun kashe mutum huɗu ciki har da ɗan sanda a wasu ƙauyuka biyu ranar Litinin.

Arewa maso gabas

Mayaƙan ISWAP sun kashe mutum uku a gundumar Kautikari da ke yankin ƙaramar hukumar Chibok a jihar Borno ranar Talata.

Harin ya faru ne lokacin da shugaban majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres, ya kai ziyara ga gwamnan jihar Borno, Fafesa Babagana Umaru Zulum.

A Gombe, bayanai sun nuna cewa matasa uku ne suka rasa rayukan su yayin da wani haɗari ya rutsa da su a wurin hawan Sallah ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Gara ku biya kuɗin fansar Fasinjojin jirgin kasa da ku sayi Fom ɗin takara a 2023, Sheikh Gumi

Arewa ta yamma

Mazauna ƙaramar hukumar Bakura a jihar Zamfara sun bayyana cewa aƙalla mutane 56 suka rasa rayukan su ranar Jumu'a da yamma lokacin da ƴan bindiga suka farmaki ƙauyuka uku a yankin.

Wani tsohon Kansila da ya nemi a ɓoye bayanansa ya ce yan ta'addan sun shiga Sabon Garin Damri da misalin ƙarfe 2:30 na rana.

Awanni 24 bayan haka, yan bindiga suka sake kashe wasu mutum 7 a yankin ƙaramar hukumar Maradun duk a Zamfara.

"Ina cikin babban Asibin Maradun lokacin da Sojoji suka shigo da gawarwakim waɗan da suka rasa rayukan su," inji wani mai suna Jamilu Muhammad.

A wani labarin kuma 'Yan bindiga sun zagaye gari a Katsina, sun kashe mutane da dama

Wasu yan bindiga sun yi nufin aikata mummunar ta'asa a kauyen Gurbin Magarya dake ƙaramar hukumar Jibiya a jihar Katsina.

Bayanai sun nuna cewa yan ta'addan sun toshe hanyoyin fita daga kauyen suka kashe mutum uku kafin Sojoji su kara so.

Kara karanta wannan

Wani Bam ya ƙara tashi mutane na tsaka da holewa a jihar Kogi, rayuka sun salwanta

Asali: Legit.ng

Online view pixel