2023: Ganduje zai siya fom din takarar sanata mai wakiltar arewacin Kano
- Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya shirya tsaf domin siyan fom din takarar sanata mai wakiltar mazabar arewacin Kano
- Zai siya fom din a ranar Litinin mai zuwa kamar yadda majiya ta tabbatar domin hayewa kujerrar Sanata Barau, na hannun damansa a baya
- Kafin ruwa yayi tsami a tsakanin Sanata Barau da Ganduje, an sakankance cewa shi gwamnan zai zaba domin maye gurbinsa bayan cikar wa'adin mulkinsa karo na biyu
Kano - Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya shirya tsaf domin siyan fom din takarar kujerar sanata mai wakiltar arewacin Kano a ranar Litinin.
Vanguard ta rahoto cewa, Ganduje ya yanke wannan hukuncin ne a taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar wanda suka yi a sirrance a gidan gwamnatin jihar.
Wata majiya mai dauke da labarin daga taron, ta ce Gwamnan zai siya fom din a ranar Litinin mai zuwa.
Da wannan cigaban, Ganduje ya shirya tsaf domin fatattakar Sanata Barau Jibrin wanda yanzu haka yake rike da kujerar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Duk da cewa, Jibrin ya bayyana cewa zai nemi takarar gwamnan jihar, amma har yanzu bai siya fom din ba.
Kafin yanzu, Jibrin na hannun daman Ganduje ne kuma ana kallonsa a matsayin wanda Ganduje zai zaba domin gadar kujerarsa kafin ruwa ya yi tsami tsakaninsu kuma ya koma tsagin APC na G7 wanda Sanata Ibrahim Shekarau yake shugabanta.
2023: Masu ruwa da tsakin APC sun yarje wa Ganduje ya nemi kujerar Barau a Kano
A wani labari na daban, masu ruwa da tsakin jam'iyyar APC na jihar Kano sun bai wa gwamna Abdullahi Umar Ganduje damar takarar Sanata na arewacin jihar Kano, Daily Trust ta tattaro.
An tattaro hakan ne, bayan yanke hukunci yayin kammala taron masu ruwa da tsaki da aka gabatar a safiyar Lahadi a gidan gwamnatin jihar Kano.
Gwamnan, wanda zai sauka daga madafun iko a watan Mayun shekara mai zuwa bayan maimaita kujerarsa, dan asalin karamar hukumar Dawakin Tofa ne, wacce ke yankin arewacin jihar Kano.
Majiyoyi da suka halarci taron sun bayyanawa Daily Trust yadda aka yarda Ganduje ya dauki yi takarar Sanata a jam'iyyar ba tare wani ya nema kujerar ba.
A halin yanzu, Sanata Barau Jibrin ne ke rike da mukamin, wanda mamba ne a tsagin G-7, sannan dan takarar gwamnan jihar.
Asali: Legit.ng