2023: Masu ruwa da tsakin APC sun yarje wa Ganduje ya nemi kujerar Barau a Kano

2023: Masu ruwa da tsakin APC sun yarje wa Ganduje ya nemi kujerar Barau a Kano

  • Masu ruwa da tsakin jam'iyyar APC na jihar Kano sun yarje wa gwamna Abdullahi Umar Ganduje kan ya yi takarar Sanata na arewacin jihar
  • An gano yadda aka yanke hukuncin nan bayan kammala taron masu ruwa da tsaki da aka gabatar a safiyar Lahadi a gidan gwamnatin jihar Kano
  • Sanata mai jiran gadon zai sauka daga kujerar gwamnan jihar a watan Mayun shekara mai zuwa, sannan zai yi takarar sanata a jam'iyyar ba tare da wani ya nemi kujerar ba

Kano - Masu ruwa da tsakin jam'iyyar APC na jihar Kano sun bai wa gwamna Abdullahi Umar Ganduje damar takarar Sanata na arewacin jihar Kano, Daily Trust ta tattaro.

An tattaro hakan ne, bayan yanke hukunci yayin kammala taron masu ruwa da tsaki da aka gabatar a safiyar Lahadi a gidan gwamnatin jihar Kano.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ganduje Ya Dira Gidan Shekarau 'Don Ƙoƙarin Hana Shi Fita Daga APC'

2023: Masu ruwa da tsakin APC sun yarje wa Ganduje ya nemi kujerar Barau a Kano
2023: Masu ruwa da tsakin APC sun yarje wa Ganduje ya nemi kujerar Barau a Kano. Hoto daga Daily Trust
Asali: Facebook

Gwamnan, wanda zai sauka daga madafun iko a watan Mayun shekara mai zuwa bayan maimaita kujerarsa, dan asalin karamar hukumar Dawakin Tofa ne, wacce ke yankin arewacin jihar Kano.

Majiyoyi da suka halarci taron sun bayyanawa Daily Trust yadda aka yarda Ganduje ya dauki yi takarar Sanata a jam'iyyar ba tare wani ya nema kujerar ba.

A halin yanzu, Sanata Barau Jibrin ne ke rike da mukamin, wanda mamba ne a tsagin G-7, sannan dan takarar gwamnan jihar.

Rikicin APC a Kano: Ɗan Majalisa, Abdulkadir Jobe Ya Fice Daga Jam'iyyar APC, Ya Bayyana Dalili

A wani labari na daban, Dan majalisar wakilai na tarayya daga Jihar Kano, Abdulkadir Jobe, ya yi murabus daga jam'iyyar ta All Progressives Congress (APC) mai mulki a kasa, Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kano: Tsohon Kwamishinan Ganduje Ya Fita Daga Jam'iyyar APC

Mr Jobe, wanda ke wakiltar mazabun Dawakin Tofa/Rimin Gado/Tofa ya ce ya fice daga jam'iyyar ne saboda rikicin cikin gida da ake yi a jam'iyyar reshen Kano.

Amma, bai bayyana cewa ko zai shiga wata jam'iyyar siyasar ba. Sai dai, an ga hotonsa da tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso na jam'iyyar NNPP bayan wata ziyara da ya kai masa a ranar Juma'a a gidansa da ke Abuja.

Mr Jobe, cikin wasikar murabus da ya aika wa shugaban jam'iyyar APC a mazabarsa ta Joben Kudu ya ce:

"Ina rubuta wannan ne domin sanar da murabus di na daga jam'iyyar APC a hukumance daga ranar Alhamis 5 ga watan Mayun 2022.
"Bayan tuntuba da magoya baya na da abokan siyasa, mun ga cewa babu amfani mu cigaba da zama a APC saboda rikicin da ke faruwa a jihar Kano a yanzu."

Asali: Legit.ng

Online view pixel